Me Ya Yi Zafi? APC Ta Sanar da Ficewa daga Zaben Ƙananan Hukumomi, Ta Jero Dalilai
- Jam’iyyar APC ta janye daga zaben kananan hukumomin Osun da aka shirya ranar 22 ga Fabrairun 2025
- APC ta dauki matakin ne saboda hukuncin kotu da ya mayar da shugabanninta ofisoshinsu
- Jam'iyyar ta ce hukuncin kotu ya tabbatar shugabanninta sun koma bakin aiki, don haka ba za ta shiga zabe ba
- Hakan ya biyo bayan barkewar rikici tsakanin APC da PDP kan wannan hukunci, inda mutane shida suka mutu, wasu suka jikkata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Jam’iyyar APC a jihar Osun ta janye daga zaben kananan hukumomi da ke shiri yi.
Jam'iyyar ta ɗauki wannan mataki ne a zaben da aka shirya yi a ranar Asabar, 22 ga Fabrairun 2025.

Asali: Facebook
Rigima ta barke kan ikon kananan hukumomi

Kara karanta wannan
Rigima ta ƙara ɗaukar zafi, ana zargin IGP da shirya kashe gwamnan PDP a Najeriya
Wannan na kunshe ne a cikin wasika da Punch ta gani mai kwanan wata 17 ga Fabrairu, wacce sakataren yada labaranta, Alao Kamorudeen, ya sanya wa hannu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rikici ya barke tsakanin APC da PDP kan hukuncin kotu da ya shafi shugabannin kananan hukumomin APC da aka kora.
PDP ta ce hukuncin Kotun Daukaka Kara na ranar 10 ga Fabrairu bai mayar da shugabannin APC ba, amma APC ta ce an mayar da su.
Rikicin ya yi kamari ranar Litinin, inda kowane bangare ya ce shi ne yake da ikon shiga ofisoshin kananan hukumomi.
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane shida tare da jikkatar wasu da dama a rikicin da ya barke, cewar Vanguard.
Wani kwafin wasikar da aka fitar a Osogbo ranar Alhamis 20 ga watan Janairun 2025 ya nuna APC ba za ta shiga zabe ba.
Musabbabin da APC ta janye daga zabe

Kara karanta wannan
'Yan Majalisa 27 sun tattara kayansu sun fice daga jam'iyyar APC? an samu bayanai
Wasikar ta ce:
“Ku tuna cewa hukuncin Babbar Kotun Tarayya a shari’a mai lamba FHF/OS/CS/94/2022 an soke shi a kotun daukaka kara, a ranar 10 ga Fabrairu, Kotun Daukaka Kara ta Akure, a shari’a mai lamba CA/AK/270/2022, ta soke wannan hukunci."
"Hukuncin ya ba zababbun shugabanni damar komawa bakin aiki kamar yadda kotu ta yanke hukunci, sakamakon wannan hukunci, kujerun shugabanni ba su sake ba, don haka ba za mu shiga wannan zabe ba."
"Dangane da haka, APC da ‘yan takararta sun sanar da hukumar zabe cewa sun janye daga zaben kananan hukumomi, saboda haka, zaben ya zama babu amfani, domin a halin yanzu ba shi da tushe a doka."
Ciyamomi a Osun sun koma ofis bayan rigima
Kun ji cewa Shugabannin kananan hukumomi karkashin APC da kansiloli a Osun sun koma ofis a kananan hukumomi 14, tare da rakiyar magoya baya.
Tsohon hadimin gwamna, Jami’u Olawumi ya ce jami’an tsaro sun kasance a yankunan da shugabannin APC suka koma.
Asali: Legit.ng