Rigima Ta Ƙara Ɗaukar Zafi, Ana Zargin IGP da Shirya Kashe Gwamnan PDP a Najeriya
- PDP ta zargi babban sufetan ƴan sanda na ƙasa na taimakawa shirin kashe gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke
- Shugaban PDP na Osun, Sunday Bisi ya ce IGP Kayode ya tura dakaru na musamman su raka ɓara garbi zuwa sakatariyar ƙananan hukumomi
- Wannan zargi na PDP na zuwa bayan rikicin da ya ɓarke da tsofaffin ciyamomi suka yi kokarin komawa bakin aiki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun - Jam’iyyar PDP reshen Osun ta zargi Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, da shirin kashe gwamnan jihar, Sanata Ademola Adeleke.
Shugaban PDP na Osun, Sunday Bisi ne ya yi wannan zargin da yake zantawa da manema labarai a Osogbo kan abubuwan da ke faruwa a jihar.

Asali: Twitter
PDP ta zargi IGP da rura wutar rikici
Sunday Bisi, ya yi ikirarin cewa Egbetokun ya tura runduna ta musamman don raka wasu bata-gari zuwa sakatariyar kananan hukumomi a jihar, rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana wannan mataki a matsayin "juyin mulki", yana mai cewa wani yunkuri ne da aka tsara don hallaka Gwamna Adeleke.
“Dole duniya ta ja kunnen IGP Kayode Egbetokun domin ya daina goyon bayan wannan mugun shiri da aka kulla domin kai wa gwamnanmu hari.
"Wannan makirci dai tun bayan da al’ummar Osun suka kayar da APC a shekarar 2022, APC ke kokarin aiwatar da shi.”
An jefa rayuwar gwamna a haɗari
Sunday Bisi ya ci gaba da cewa:
“Rikicin da APC ke haddasawa na ƙara dagula komai. Saboda haka, duk wani abu da ya faru a jihar Osun, a tuhumi Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da alhakin hakan.”
“Abin mamaki ne yadda IGP Egbetokun ya manta da matsayi na gwamna, duk da shi ne babban jami’in tsaro na jihar amma ake masa wannan cin kashin. Wannan raina doka ne."

Asali: Facebook
PDP ta caccaki IGP da take doka
Jam'iyyar PDP ta kuma zargi IGP Egbetokun da bijirewa dokokin tsaro, yana mai cewa hakan na iya haddasa tashin hankali a Osun.
Jam’iyyar ta koka cewa a cikin saa’i 48 kacal, mutane 10 sun rasa rayukansu sakamakon tashe-tashen hankula, tana mai cewa tura karin jami’an tsaro zai bai wa bata-gari damar aikata mummunan laifi.
Ciyamomin APC sun koma bakin aiki
A wani labarin, kun ji cewa ciyamomin APC da kansiloli a kananan hukumomi 14 sun sake komawa ofis bayan rikicin da ya faru har aka rasa rayuka a Osun.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an girke tulin jami'an tsaro a kowace saƙatariyar karamar hukuma da shugabannin suka koma aiki don ba su tsaro.
Asali: Legit.ng