Malamin Addini Ya Shiga Siyasa a Kano, Ya Jagoranci Magoya Bayansa Zuwa Jam'iyyar APC
- Sanata Barau Jibrin ya karɓi shugabannin addini, ‘yan siyasa da matasa daga NNPP a Kano, waɗanda suka sauya sheka zuwa APC
- Jagoran Qadiriyya Riyadul Jannah a Getso, Malam Abubakar Mai Kanzu ya goranci daruruwan mabiyansa zuwa jam'iyyar APC
- Alhaji Ade ya yaba da kafa cibiyoyin NOUN a Kano ta Arewa, da ginin makarantar NSCDC da filin wasa domin ci gaban matasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karbi 'yan NNPP na jihar Kano da suka sauya sheka zuwa APC.
Sanata Barau Jibrin ya ce ya kuma karbi wasu shugabannin addini da na gargajiya, malaman boko da kusoshin siyasa daga karamar hukumar Gwarzo.

Asali: Twitter
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a yau ranar Laraba, Sanata Barau ya ce ya karbi masu sauya shekar ne a ofishinsa da ke zauren majalisar tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jagoran darikar Qadiriyya ya shiga jam'iyyar APC
Sanarwar Sanata Barau ta ce:
"Na karɓi wata ƙungiya daga Getso a ƙaramar hukumar Gwarzo, wacce ta ƙunshi shugabannin addini da na gargajiya, shugabannin jam’iyya, malamai, ‘yan siyasa na ƙasa da matasa waɗanda suka shiga jam’iyyar APC a hukumance.
"Daga cikinsu har da Malam Abubakar Mai Kanzu, Muqaddam na Qadiriyya Riyadul Jannah a Getso, wanda ya shiga APC tare da ɗaruruwan mabiyansa.
"Haka kuma, Zubairu Halilu Getso, wani matashin ɗan siyasa a matakin ƙasa, ya jagoranci magoya bayansa zuwa APC bayan gazawar gwamnatin NNPP a Kano wajen cika alƙawuran da ta ɗauka a zaɓe.
"Ya nemi a kammala ginin ofishin ‘yan sanda da kasuwa a yankinsu, tare da gyaran madatsar ruwa ta Getso don farfaɗo da noman rani.
"Na tabbatar masa da jajircewata wajen gyaran madatsar ruwan da kammala ofishin ‘yan sanda don ƙarfafa tsaro da bunƙasa harkar noma a yankin Getso."
Matasan Gwarzo a Kano sun koma APC
Sanata Barau ya kuma ce wasu matasan Gwarzo karkashin kungiyar GYA, bisa jagorancin Alhaji Sadisu Aliyu Ibrahim wanda aka fi sani da Alhaji Ade Gwarzo sun koma APC.
Mataimakin shugaban majalisar ya ce wadanda suka sauya shekar sun shaida masa cewa sun gamsu da ayyukan gwamnatin APC ya sa suka shiga jam'iyyar.
"Alhaji Ade ya yaba da shirin mu na faɗaɗa damar samun ilimin jami'a ta hanyar kafa cibiyoyin karatu na jami'ar NOUN a ƙananan hukumomi 13 na yankin Sanatan Kano ta Arewa.
"Haka kuma, ya jinjina man kan ginin makarantar horas da jami’an NSCDC da filin wasa a Gwarzo, wanda ya ce zai bai wa matasa dama su shiga harkokin wasanni da ayyukan ci gaban al’umma."
- Sanata Barau Jibrin.
Kano: Jarumi Nabraska ya fice daga NNPP
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jarumin Kannywood, Mustapha Nabraska, ya fice daga NNPP da Kwankwasiyya, inda ya koma APC bayan jefar da jar hularsa a Abuja.

Kara karanta wannan
PDP ta soki 'yan majalisar da su ka sauya sheka, ta fara kokarin raba su da mukamansu
A yayin sanar da ficewarsa, ya bayyana dalilansa, lamarin da ya janyo cece-kuce tsakanin magoya bayansa, wasu na goyon baya yayin da wasu ke sukar matakin.
Masu sharhi kan siyasa sun bayyana cewa sauyin shekarsa ka iya zama alamar rikici a Kwankwasiyya, yayin da APC ke ci gaba da karɓar sabbin ‘yan jam’iyya.
Asali: Legit.ng