"Allah Ne Ya Jarabe Mu," Gwamna Ya Faɗawa Babban Malami Abin da Bai Sani ba

"Allah Ne Ya Jarabe Mu," Gwamna Ya Faɗawa Babban Malami Abin da Bai Sani ba

  • Gwamna Siminalyi Fubara ya ce Allah ya jaraba jihar Ribas da rikicin cikin gida ba don komai ba sai dan ya ba al'ummarta cikakken ƴanci
  • Fubara, wanda ke faɗa da ubangidansa a siyasa, Nyesom Wike ya faɗi haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin babban limamin cocin Anglican a Fatakwal
  • Ya bayyana cewa gwamnatinsa tana tafiya ne a kan tafarkin da Allah ya tsara mata, yana mai ƙara godewa babban malamin bisa ƙoƙarin sulhun da ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa Allah ya jarabci jihar da rikicin siyasar da ake fama da shi ne domin mutane su samu ƴanci.

Fubara ya yi wannan furuci ne a ranar Talata da babban limamin cocin Anglican na Najeriya, Henry Ndukauba, tare da wasu shugabannin coci, suka kai masa ziyara a fadar gwamnati da ke Fatakwal.

Kara karanta wannan

"Ba sabani aka ba," Naburaska ya fadi dalilin watsi da Kwankwasiyya

Gwamna Siminalayi Fubara.
Dalilin da ya sa Allah ya bar rikicin siyasar jihar Ribas ya yi tsanani, in ji Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Fubara ya tuna da kokarin da babban limamin Anglican ya yi tun farko don kawo karshen rikicin siyasar da ake fama da shi a jihar Ribas, kamar yadda The Nation ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya faɗi dalilin yaɗuwar rikici

Da yake magana da babban limamin, gwamnan ya ce:

"Ina so na fara da miƙa godiya ta musamman ga babban malaminmu. Wataƙila wasu ba za su fahimci dalilin godiyata ba."
"Tun farkon wannan rikici, a matsayinsa na malamin addini wanda ya san cewa dukkan bangarorin da ke rikicin sun fito daga cocinsa, ya yi kokarin sulhunta mu.
"Ya shirya ganawa da bangarorin biyu, amma ba a ba shi dama ba. Saboda haka, ina so na gode maka, duk da ba a yi sulhu ba amma ka san Shi Allah yana da hanyoyin gudanar da al’amura.
"Wataƙila da sulhu ya samu tun farko, da ba zan samu ‘yancin da nake morewa a yau ba."

Kara karanta wannan

Gwamna ya kwaikwayi Abba Kabir na Kano, ya rabawa mata awaki 40,000

Zaman lafiya ne tushen ci gaba

Gwamnan ya jaddada cewa ko da yake wasu lokuta rikici yana zama hanyar samun nasara, hakan ba yana nufin yana son rigima a ko da yaushe ba ne.

"Zaman lafiya shi ne hanya mafi dacewa wajen kawo ci gaban kowace al’umma, kuma shi ne kadai zai iya kawo ci gaba da hadin kai a kasa," in ji shi.

Fubara ya bayyana farin cikinsa da babban taron cocin Anglican wanda ke gudana a jihar Rivers.

Gwamnatin Ribas na bukatar addu'o'i

Ya ƙara da cewa wannan taron ya zo a daidai lokacin da gwamnatinsa ke bukatar addu’o’i don cigaba da tafiya bisa tafarki na adalci.

Gwamna Fubara ya ce Allah ne ke jan ragamar harkokin gwamnatinsa kuma ba zai yarda a ɗora masa ƙarfin iko da yabon da ya dace da Ubangiji ba.

Ya tabbatar wa shugabannin addinin cewa gwamnatinsa ba za ta taba kaucewa bin hanyar Allah ba kuma za ta ci gaba da tallafa wa ayyukan addini a jihar.

Kara karanta wannan

Cikin sarakuna ya ɗuri ruwa, gwamna ya yi barazanar tsige su daga kan sarauta

Kotu ta kori ƙarar Gwamna Fubara

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Fubara ya yi rashin nasara a ƙarar da ya shigar gaban kotun ƙoli kan sauya sheƙar ƴan Majalisa 27.

Kotu mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta kori ƙarar kana ta ci tarar gwamnan Naira miliyan 2 bayan waɗanda ake ƙara sun miƙa buƙatarsu ga alƙali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262