"Menene Hujjar Ku?" PDP Ta Karyata Kitsa Kai wa APC Hari a Zamfara

"Menene Hujjar Ku?" PDP Ta Karyata Kitsa Kai wa APC Hari a Zamfara

  • Jam’iyyar PDP ta musanta zargin APC cewa ta ɗauki hayar ƴan daba don kai hari ga membobin jam’iyyar a wani taro da aka gudanar a Zamfara
  • PDP ta kalubalanci APC da ta bayyana sunayen wadanda suka dauki nauyin harin da kuma tabbatar da cewa su mambobin PDP ne kafin jama’a su amince
  • PDP ta yi kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki mataki kan ɗan majalisar wakilai Abdulmalik Zubairu, wanda aka ce ya shirya taron da ba bisa ƙa’ida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta musanta zargin da jam’iyyar adawa ta APC ta yi cewa ta ɗauki hayar ƴan daba don kai hari ga membobinta a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

PDP ta soki 'yan majalisar da su ka sauya sheka, ta fara kokarin raba su da mukamansu

Jam’iyyar PDP ta kalubalanci APC da ta gabatar da hujjoji da za su gamsar da al’ummar Zamfara cewa wannan zargin ta na da hannun a harin gaskiya ne.

Dauda Lawal
PDP ta musanta hari kan 'yan APC a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

A wani labari da ya kebanta ga talabijin na AIT, jPDP ta bayyana cewa babu wata sahihiyar hujja da ke alakanta da da kai farmaki a kan taron jam'iyyar hamayya a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zamfara: PDP ta kalubalanci APC

Jam’iyyar PDP ta kalubalanci APC da ta gabatar da hujjoji da shaidun da za su alakanta da kitsa harin da aka kai wa 'ya'yan jam'iyyar a ranar 15 ga Fabarairu, 2025.

PDP ta bukaci APC ta bayyana sunayen membobin PDP da suka dauki nauyin harin, sannan ta tabbatar mata da cewa wadanda suka kai harin, mambobin jam'iyyarta ne.

Jam’iyyar ta gargadi jama’a da kada su karɓi kowanne zargi daga APC sai sun gabatar da shaidu a gaban kotu mai ƙwarewa da za ta yanke hukunci.

Kara karanta wannan

APC ta yi raddi ga Tambuwal, ta fadi dalilin raba garinsa da jam'iyyar

PDP ta nemi a hukunta ɗan majalisar APC

PDP ta yi kira ga APC da ta yi magana da shugabancinta a jihar da kuma ɗan majalisar wakilai, Abdulmalik Zubairu, wanda ya shirya wani taron da jam’iyyar ke ganin ba bisa ƙa’ida ba a garin Bungudu.

PDP ta tabbatar wa al’ummar jihar Zamfara cewa, za ta matsa kaimi kan hukumomin tsaro su ɗauki mataki kan Abdulmalik Zubairu idan an samu wata matsala ta rashin tsaro da ta biyo bayan taron da ya shirya.

PDP ta tunatar da APC cewa, yanzu ba lokacin yakin neman zaɓen 2027 ba ne, don haka ta bar al’ummar Zamfara su zauna cikin zaman lafiya.

Mazauna Zamfara sun yi zanga-zanga

A baya, kun ji cewa Mazauna garin Maru na jihar Zamfara sun fito kan tituna don yin zanga-zanga sakamakon ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga da suka ce yana jefa rayuwarsu a dawuwa.

Mutanen sun nuna ɓacin ransu ta hanyar toshe manyan hanyoyi da ke haɗa Gusau da Sokoto, wanda ya hana zirga-zirgar ababen hawa a wannan yankin bayan sabon hari da aka kai garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.