APC Ta Yi Raddi ga Tambuwal, Ta Fadi Dalilin Raba Garinsa da Jam'iyyar
- Jam’iyya mai mulki ta APC ta ce tsohon gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya fi kowa yawan sauya jam’iyya don biyan bukatun kansa.
- A ranar asabar ne tsohon gwamnan Sakkwato ya ce babu ɗan siyasa mai hankali da zai shiga APC, yana mai zargin masu sauya sheƙa da son rai
- APC ta ce waɗanda ke shiga jam’iyyar su na yin hakan ne domin su goyi bayan manufofin gyaran tattalin arzikin Shugaba Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja — Jam’iyya mai mulki ta APC ta mayar da martani kan furucin da tsohon gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya yi game da masu sauya sheka zuwa cikinta.
Tambuwal ya ce babu wani ɗan siyasa da ya san ciwon kansa da zai shiga APC, yana mai cewa waɗanda ke komawa jam’iyyarm suna yin hakan ne saboda biyan bukatar kashin kai.

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa tsohon gwamnan ya ce halin da tattalin arzikin ƙasa ke ciki a yanzu, ya na hana mutane sha’awar shiga APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya fadi haka ne a ranar Asabar a Kaduna, bayan taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) na PDP na yankin Arewa maso Yamma.
Martanin APC ga Tambuwal
Daily Trust ta wallafa cewa Felix Morka, mai magana da yawun APC, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya siffanta tsohon gwamnan Sakkwato a matsayin shahararren mai sauya jam'iyya.
Morka ya ce kalaman Tambuwal sun bayyana halinsa ne kawai, domin yawan sauya jam'iyya da ya ke yi, ba don komai ba ne sai don cikinsa.
Ya ce:
“Ɗan siyasar da ke yawo daga wannan jam’iyya zuwa waccan kamar Tambuwal ba shi da wata nagarta ta ɗabi’a da zai yi tsokaci kan dalilan ‘yan siyasa da suka bar PDP mai cike da rikici suka shigo babbar jam’iyyarmu.”
APC ta fadi masu komawa cikinta
Mai magana da yawun APC ya bayyana cewa waɗanda ke shiga jam’iyyar mai mulki suna yin hakan ne don sun amince da tsarin tattalin arzikin Bola Ahmed da ke kawo ci gaba da Najeriya.
Ya ce:
“A bayyane yake, furucinsa ya fi dacewa da tarihin sauya sheƙarsa daga jam’iyyar ANPP zuwa DPP a 2007, sannan ya koma ANPP, daga nan ya wuce PDP, ya sauya sheƙa zuwa APC a 2014, kafin daga bisani ya koma PDP cikin rashin mutunci a 2018.”
“Dangane da ikirarinsa, sauya-sheƙar Tambuwal daga wannan jam’iyya zuwa waccan yana da nasaba da ‘son cikinsa,’ ba tare da wata sanin ya kamata ba.”
“Sabanin abin da Tambuwal ya faɗa, ‘yan PDP na komawa APC ne domin su kasance tare da shirin gyaran tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu, a yayin da alamomi masu kyau ke ƙaruwa waɗanda ke nuna cewa Najeriya na farfaɗo wa.”

Kara karanta wannan
"Kwankwaso na kamun kafa don dawo wa jam'iyyarmu," APC ba ta bukatar jagoran NNPP
Tambuwal ya dira a kan APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa 'yan siyasar da ke koma wa cikin APC na yin haka ne domin biyan bukatar kansu.
Tambuwal ya kara da cewa masu yin hakan ba su da tausayi, domin halin da Najeriya ta ke ciki a yanzu bai dace ya ba wani dan siyasa mai kishi sha'awar da zai koma cikin jam'iyya mai mulki ba.
Asali: Legit.ng