'Ba Ka Ji Kunya ba': An Yi Wa Uba Sani Shagube da Ya Tura Sako ga El Rufai
- Gwamna Uba Sani na Kaduna ya taya Nasir El-Rufai murnar zagayowar haihuwarsa, yana mai masa fatan alheri da kariya daga Allah madaukaki
- Wannan sakon taya murnar ya biyo bayan rade-radin rashin jituwa tsakaninsu, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta
- Wasu sun ce Uba Sani ya ci amanar El-Rufai, yayin da wasu ke ganin hakan ya dace don nuna kwarewa a siyasa ba tare da gaba ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jiahr Kaduna - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yi wa tsohon gwamna, Nasir El-Rufai fatan alheri.
Uba Sani ya taya tsohon gwamnan murnar zagayowar ranar haihuwarsa bayan ya cika shekaru 65.

Asali: Twitter
Mutane sun nuna bambancin ra'ayi kan sanarwar
Uba Sani ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a yau Lahadi 16 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan zargin rigima tsakanin Uba Sani da mai gidansa da ke neman ɗaiɗaita APC a jihar.
Wannan sakon Uba Sani ga El-Rufai ya jawo ka-ce-na-ce a kafofin sadarwa inda mutane ke bayyana ra'ayinsu kan haka.
Mafi yawan wadanda suka yi tsokaci sun bayyana cewa ya kamata Uba Sani ya ji kunya bayan cin amanar Nasir El-Rufai.
A daya bangaren, wasu na ganin hakan ne ya dace a rika siyasa ba da gaba na domin kawo ci gaba a cikin al'umma.
Uba Sani ya taya El-Rufai murna
A cikin sakon taya murnar, Uba Sani ya ce:
"Ina mika gaisuwar taya murna da fatan alheri ga dan'uwana, abokina kuma magabaci na, Mai Girma Malam Nasir El-Rufai CON, a bikin zagayowar ranar haihuwarsa da shekaru 65.
"Ina rokon Allah madaukaki ya ci gaba da shiryar da shi, ya kare shi, ya kuma kara masa ƙarfi."
Martanin masu amfani da kafar sadarwa:
@Alhajiabumaiqo:
"A dai rika yi ana hadawa da kunya ko ba komai a kan iya kiranka dattijo ko ta bangaren shekaru."
@Talk2MaRa:
"Ka gaza kiransa a matsayin mai gidanka."
@interflex2004:
"Wannan shi ne girma Mr Gwamna, ka kasance na daban."
@onmamien:
"Siyasa ba da gaba ba, ka kasance mai hada kan al'umma."
@abubillaal:
"Don Allah ba ka ji kunyar yin wannan rubutu ba?"
Tinubu ta taya El-Rufai murnar cika shekaru 65
Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya taya tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Shugaban ya yi masa fatan alheri duk da sukar da El-Rufai ya rika yi masa da kuma jam'iyyarsa ta APC a yan kwanakin nan.
Asali: Legit.ng