Tambuwal Ya Dura kan Gwamnatin APC, Ya Yi Wa 'Yan Siyasa Tonon Silili

Tambuwal Ya Dura kan Gwamnatin APC, Ya Yi Wa 'Yan Siyasa Tonon Silili

  • Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya caccaki ƴan siyasa masu sauya sheƙa daga wannan jam'iyya zuwa waccan
  • Tambuwal ya bayyana cewa ƴan siyasar da suke yin hakan, su na yi ne kawai don cimma buƙatunsu ba don al'umma ba
  • Tsohon gwamnan ya kuma caccaki gwamnatin APC, inda ya nuna cewa babu tausayi a yadda take gudanar da mulki a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya yi magana kan yawan sauya sheƙar da ƴan siyasa suke yi a yankin Arewa maso Yamma.

Tambuwal ya yi watsi da yawan sauya sheƙar, yana mai cewa sauya jam’iyyar ba don amfanin al’umma ake yi ba, sai dai don cimma buƙatu ƙashin kai.

Tambuwal ya caccaki 'yan siyasa
Tambuwal ya caccaki 'yan siyasa masu sauya sheka Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Twitter

Tambuwal ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana da manema labarai bayan taron farko na kwamitin zartarwa na PDP na shiyyar Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kaduna a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Buhari ya fadi laifin da Tinubu ya yi wa manyan Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tambuwal ya soki masu komawa APC

Tsohon gwamnan ya soki masu komawa jam’iyyar APC mai mulki, yana mai cewa ba domin al'umma suke yin hakan ba, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Mutane suna barin jam’iyyunsu ne saboda dalilai daban-daban. Amma abin da na lura da shi shi ne, yawancin sauya sheƙa ba don buƙatar talakawa ake yi ba, sai don buƙatun ƙashin kai, wato don su gyara tukunyarsu."
"Idan kai ɗan siyasa ne mai tunani da tausayi, ba za ka koma APC ba duba da halin matsin tattalin arziki da kuma gazawar gwamnatin Tinubu."

- Aminu Waziri Tambuwal.

Tsohon shugaban na majalisar wakilai ya zargi gwamnatin APC da rashin shugabanci nagari, yana mai cewa babu tsari ko tausayi a yadda take tafiyar da mulki.

Wace shawara ya ba ƴan adawa?

Aminu Tambuwal ya buƙaci jam’iyyun adawa su haɗe kansu domin fuskantar zaɓen 2027, don samarwa ƴan Najeriya wata jam'iyya mai ƙarfi wacce ba APC ba.

Kara karanta wannan

Tinubu: Dan majalisa ya hada Ganduje da El Rufa'i, ya gyara musu zama kan 2027

"Babu wani abin burgewa a APC face son cimma buƙatar ƙashin kai. Mu da muka ƙudiri aniyar yi wa al’umma aiki, dole ne mu haɗe don tabbatar da cewa a 2027 mun kawar da wannan gwamnatin da ta ci amanar ƴan Najeriya."

- Aminu Waziri Tambuwal

PDP ta shirya dawowa kan mulki

A gefe guda, jam'iyyar PDP ta shiyyar Arewa maso Yamma ta jaddada aniyarta ta dawowa kan mulki a 2027, tana mai cewa dole ne a haɗa kai domin cin nasara.

A wata sanarwa da aka fitar bayan taron, shugaban PDP na Arewa maso Yamma, Sanata Bello Hayatu Gwarzo, ya jaddada cewa jam’iyyar ta shirya tsaf don sake karɓar ragamar mulkin ƙasar nan.

Tambuwal ya caccaki Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ƙudirin haraji.

Tambuwal ya caccaki shugaban ƙasan kan gabatar da ƙudirin a gaban majalisa, inda ya bayyana cewa ba yanzu ba ne lokacin da ya kamata a kawo shi ba, duba da halin matsin da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng