Ana Batun Kawar da Shi a 2027, Kungiyar APC Ta Yi Wa Tinubu Alkawarin Ruwan Kuri'u

Ana Batun Kawar da Shi a 2027, Kungiyar APC Ta Yi Wa Tinubu Alkawarin Ruwan Kuri'u

  • Ƙungiyar APC ta yankin Arewa ta Tsakiya ta gamsu da kamun ludayin mulkin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
  • Shugaban ƙungiyar Saleh Zazzaga ya ɗaukarwa Shugaba Tinubu alƙawari kan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027
  • Ya bayyana cewa ƙungiyar ta yi wa Tinubu alƙawarin ƙuri'u miliyan huɗu domin ya zarce wa'adi na biyu kan madafun ikon Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar APC ta yankin Arewa Ta Tsakiya ta yi wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu alƙwari kan zaɓen 2027.

Ƙungiyar ta APC ta yi alƙawarin samar da ƙuri’u miliyan huɗu ga shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, domin tabbatar da cewa ya zarce wa’adi na biyu a kan mulki.

Kungiyar APC ta yi wa Tinubu alkawari
Kungiyar APC ta yi wa Tinubu alkawarin kuri'u a 2027 Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa ƙungiyar ta fitar bayan taron masu ruwa da tsakinta da aka gudanar a ranar Laraba a birnin Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya dawo daga rakiyar Tinubu, ya fadi babbar nadamar da ya yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ƙungiyar APC ke goyon bayan Tinubu?

Jagoran ƙungiyar, Saleh Zazzaga, ya ce goyon bayan da suke bai wa Tinubu alama ce ta girmama yadda yake jagorantar ƙasar nan duk da adawar da a ke yi masa.

Zazzaga ya danganta goyon bayansu ga Tinubu kan yadda ya bai wa yankin muƙamai masu mahimmanci a cikin majalisar zartarwa, ta hannun shugabancin jam’iyyar APC wacce Ganduje ke jagoranta.

Ƙungiyar ta yaba da ci gaba da yin ayyukan raya ƙasa a yankin, ciki har da titin Suleja-Minna-Bida da titin Akwanga-Keffi-Plateau-Gombe.

Ƙungiyar ta yarda da shugabancin Ganduje

Har ila yau, ƙungiyar ta sake tabbatar da goyon bayanta ga shugabancin Abdullahi Umar Ganduje, tana mai jaddada cewa ƙwarewarsa ta dace ya ci gaba da jagorantar jam’iyyar APC har zuwa zaɓen 2027.

Duk da cewa a baya ƙungiyar ta nuna adawa da zamansa a matsayin shugaban jam’iyyar, a halin yanzu ta dawo tana mara masa baya.

Kara karanta wannan

Ganduje ya ba 'yan Arewa shawara kan yin takara da Tinubu a zaben 2027

Ta yi watsi da raɗe-raɗin cewa naɗin da aka yi masa a matsayin shugaban hukumar kula da filayen jiragen sama ta tarayya (FAAN) wani shiri ne na cire shi daga muƙaminsa na shugabancin APC.

Saleh Zazzaga, wanda 'dan kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu a 2023 ne, ya bayyana cewa a ƙarƙashin shugabancin Ganduje, yankin Arewa-Ta Tsakiya ya samu tagomashi, aka biya musu kimamin kaso 80% na buƙatunsu da koke-kokensu.

Jigo a APC ya yi nadamar goyon bayan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC a jihar Kano, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda, ya dawo daga rakiyar Bola Ahmed Tinubu.

Alhaji Ɗan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa ya yi nadamar tallata Tinubu a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel