Jigon APC Ya Dawo daga Rakiyar Tinubu, Ya Fadi Babbar Nadamar da Ya Yi

Jigon APC Ya Dawo daga Rakiyar Tinubu, Ya Fadi Babbar Nadamar da Ya Yi

  • Jigo a jam'iyyar APC daga jihar Kano, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda, ya yi magana kan mulkin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
  • Ɗan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa ya yi nadamar yaƙin neman zaɓen da ya yi wa Shugaba Tinubu a zaɓen shekarar 2023
  • 'Dan siyasar ya bayyana cewa ƴan Najeriya sun tsinci kansu a cikin mawuyacin hali a ƙarƙashin mulkin shugaba Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Ɗan siyasa daga jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar APC, Alhaji Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda, ya yi magana kan mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Dan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa ya yi nadamar yi wa Bola Tinubu kamfen a zaɓen 2023.

Dan Bilki Kwamanda ya yi nadamar zaben Tinubu
Dan Bilki Kwamanda ya ce ya yi nadamar zaben Bola Tinubu Hoto: Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jigon na jam'iyyar APC ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Alamu sun ƙara karfi, gwamna na shirin neman takarar shugaban ƙasa a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me jigon jam'iyyar APC ya ce kan Tinubu?

Ɗan Bilki Kwamanda ya ce bisa la’akari da alamomin da suka bayyana ga kowa, Shugaba Tinubu ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka ga yawancin ƴan Najeriyan da suka zaɓe shi a 2023.

Ya bayyana cewa a gaba ɗaya rayuwarsa, bai taɓa yin nadama kan wani abu ba kamar yadda yake nadamar kamfen ɗin da ya yi wa shugaba Tinubu.

"Abin akwai ciwo, amma gaskiya ce dole a faɗa. Ni mamba ne mai aiki tuƙuru a jam’iyyar APC, amma dole na aminta da cewa mulkin Najeriya a ƙarƙashin APC ya gaza."
"A matsayina na wanda ya sadaukar da lokacinsa da dukiyarsa wajen shawo kan mutane su zaɓi jam’iyyar, dole na bayyana cewa ina nadamar yin hakan da na yi."

- Abdulmajid Ɗan Bilki Kwamanda

Ɗan Bilki Kwamanda ya nemi afuwa

Ɗan Bilki Kwamanda ya ƙara da cewa a matsayinsa na wakilin talakawa, yana buƙatar su yafe masa, domin abubuwan APC ta gaza cika abubuwan da ya alƙawarta musu.

Kara karanta wannan

Ganduje ya ba 'yan Arewa shawara kan yin takara da Tinubu a zaben 2027

Ya bayyana cewa ƴan Najeriya na cikin mawuyacin hali, domin abubuwan da suka yi tsammani daga gwamnatin APC ba su samu ba.

"Ƴan Najeriya na cikin yunwa da fushi. Ba su da kwanciyar hankali, babu cikakken tsaro, kuma salon mulki ya zama na son zuciya. Mutane ba su iya samun abinci sau biyu a rana."

- Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda

Kwamanda ya caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar APC, Abdulmajid Ɗan Bilki Kwamanda, ya caccaki tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Alhaji Ɗan Bilki Kwamanda ya bayyana tsohon gwamnan na jihar Kano a matsayin butulu a siyasa wanda bai kamata a ji tsoronsa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel