"Ta Kare Maka": Ganduje Ya Fadi Gwamnan da Zai Rasa Kujerarsa a 2025
- Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya aika saƙo ga gwmanan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo
- Ganduje ya bayyana cewa lokaci ya yi da mulkin gwamnan na jam'iyyar APGA zai zo ƙarshe a jihar ta yankin Kudu maso Gabas na Najeriya
- Shugaban na APC ya faɗi hakan ne yayin buɗe sabuwar sakatariyar jam'iyyar gabanin zaɓen fidda gwanin gwamnan da za a yi a jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Anambra - Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, tare da mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na ƙasa (NWC), sun je jihar Anambra.
Abdullahi Umar Ganduje bayyana cewa mulkin Gwamna Chukwuma Soludo da jam’iyyar APGA a jihar Anambra ya zo ƙarshe.

Source: Facebook
Ganduje da sauran mambobin NWC sun isa jihar Anambra ne domin shirin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da kuma zaɓen gwamna da za a gudanar a ranar 8 ga watan Nuwamba, cewar rahoton jaridar The Nation.
Ganduje na son ƙwace Anambra a hannun Soludo
Ziyarar tasu ta zo daidai da ƙaddamar da sabuwar sakatariyar APC ta jihar da Sir Paul Chukwuma ya samar, Farfesa Obiora Okonkwo ya sanyawa kayan aiki, rahoton Premium Times ya tabbatar.
Chukwuma da Okonkwo na daga cikin ƴan takarar neman tikitin APC domin yin takarar gwamna, tare da Prince Nicholas Ukachukwu da wasu mutum biyu.
Ƙaddamar da ofishin wanda Ganduje da tawagarsa suka yi, ya ɗauki sabon salo kamar gangamin siyasa, inda masu jawabi daban-daban suka jaddada cewa ya zama dole a kawo ƙarshen mulkin APGA a Anambra.
Yayin da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar, Ganduje ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa manufofin tattalin arziƙi da yake aiwatarwa, tare da ƙarfafa ƴan takarar APC da su haɗa kai domin ƙwace mulki daga APGA.
"Muna tabbatar muku cewa shugabanmu, Asiwaju Bola Tinubu, a matsayinsa na jagora mai hangen nesa da ƙwazo, yana da cikakkiyar masaniya kan abin da ya kamata a yi a kowane lokaci."

Kara karanta wannan
Rikicin jam'iyyar Kwankwaso ya ƙara ɗaukar zafi, sabon shugaban NNPP na ƙasa ya bayyana
"Anambra dole ne ta haɗa kai da gwamnatin tarayya. APC dole ne ta canza labarin siyasar Anambra, amma dole ne mu kasance masu mayar da hankali da faɗakarwa."
- Abdullahi Umar Ganduje
Kwankwaso ya gana da tsohon gwamnan APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa madugun Kwankwasiyya kuma jagora a jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola.
Kwankwaso ya gana da Aregbesola ne bayan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sanar da korarsa daga cikinta.
Asali: Legit.ng
