'Yan APC Sun Nunawa Kwankwaso Yatsa kan Batun Komawa Jam'iyyar
- Ƙungiyar NAGG ta APC ta yi magana kan batun cewa Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa jam'iyya mai mulki a Najeriya
- Sakataren ƙungiyar ya bayyana cewa ko babu Kwankwaso, APC a shirye ta ke ta ƙwato mulkin Kano daga hannun Abba Kabir Yusuf
- Kwamared Auwal Shuaib ya kuma nuna cewa cikin sauƙi shugaban ƙasa Bola Tinubu zai lashe zaɓe a 2027, zai doke 'yan hamayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Sakataren ƙungiyar NAGG ta jam'iyyar APC, kwamared Auwal Shuaib, ya bayyana cewa zaɓen 2027 zai kasance mai sauki ga APC da ɗan takararta, shugaba Bola Tinubu.
Ya yi amanna kan cewa jam'iyyun adawa sun shiga ruɗani don haka ba su da wani kataɓus da za su iya yi.

Source: Facebook
Kwamared Auwal Shuaib ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a Kano, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan
"Gwamna da abokin takarar Atiku na roƙon a bari su shigo APC," Sanata ya ce babu wurinsu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan APC ba su buƙatar Kwankwaso a jam'iyyar
Sakataren na ƙungiyar NAGG ya kuma yi magana kan raɗe-raɗin cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso, na shirin komawa jam'iyyar APC.
Ya bayyana cewa ko babu goyon bayan Kwankwaso, APC ta shirya karɓo mulkin jihar Kano daga hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kwamared Auwal Shuaib ya nanata cewa zaɓen 2027 zai kasance mai sauƙi ga APC da ɗan takararta, shugaba Bola Ahmed Tinubu.
APC ta nuna ƙwarin gwiwa kan nasarar Tinubu
“APC a Kano da yankin Arewa maso Yamma ba su maraba da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Muna roƙon Shugaba Tinubu da ka da ya bari a ruɗe shi."
"APC za ta samu nasara kasancewar Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyya na ƙasa. Ya nuna kyawawan halaye na shugabanci wajen tafiyar da jam'iyya da kuma iya lashe zaɓe."
“Idan aka duba sakamakon zaɓe na baya, Shugaba Tinubu ya samu sama da ƙuri'u 500,000 a Kano. Sanata Kwankwaso ya wuce shi ne da tsirarun ƙuri'u."
“Bambancin bai da wani muhimmanci idan aka duba yadda APC ta fuskanci ƙalubale. Idan har a lokacin shugaba Tinubu ya yi nasara, ba tare da goyon bayan Kwankwaso ba, to, yaya kuma yanzu da ya zama shugaban ƙasa?
“Abu mafi kyau da za a yi shi ne, a tabbatar da Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyya, da kuma ƙarfafa APC a Kano da sauran jihohi don tabbatar da nasara."
- Kwamared Auwal Shuaib
Ƙusa a APC ya gargaɗi Tinubu kan Kwankwaso
A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ja kunnen Bola Tinubu da jam'iyyar APC.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da jam'iyyar APC su yi taka tsan-tsan kan shirin Rabiu Musa Kwankwaso na komawa jam'iyyar.
Ya bayyana cewa yunƙurin da tsohon gwamnan na Kano ke yi na komawa APC, ba komai ba ne fa ce tsabar makirci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
