'Munafurcin Siyasa ba na Irinmu ba ne': El Rufai Ya Sake Ta da kura, Ya Jaddada Matsayarsa

'Munafurcin Siyasa ba na Irinmu ba ne': El Rufai Ya Sake Ta da kura, Ya Jaddada Matsayarsa

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce bai iya wasa ba a siyasa kuma ba zai zama kamar yan wasan kwaikwayo a gwamnati ba
  • El-Rufai ya bayyana hakan ne a martaninsa kan wani rubutu a dandalin sada zumunta da ke yabawa salon shugabancinsa mai gaskiya da rikon amana
  • Ya ce ba zai taɓa goyon bayan APC idan ta kauce daga tsarinta ba, ko da ko yana cikin gwamnati ko a’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kaduna - Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sake ta da hazo kan halayen wasu yan siyasa na munafurci.

El-Rufai ya ce ba ya wasa a siyasa kuma ba zai zama kamar waɗanda ke yin wasan kwaikwayo a gwamnati ba.

El-Rufai ya jaddada matsayarsa kan APC da gwamnatin Tinubu
Nasir El-Rufai ya ce kwata-kwata shi bai saba da munafurcin siyasa ba. Hoto: Nasir El-Rufai.
Asali: Facebook

Abin da hada El-Rufai, yan APC cacar baki

El-Rufai ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a martaninsa kan wata wallafa a shafin X da ke yabawa salon shugabancinsa mai gaskiya.

Kara karanta wannan

Yayin da ake shirin zaben gwamna, an fadi shirin APC domin kwace mulki cikin sauki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martaninsa ya zo ne yayin da ake ta rikici tsakaninsa da wasu jami’an gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan yadda ake tafiyar da mulki.

El-Rufai ya zargi jam’iyyar APC da kaucewa akidarta, yana mai cewa ba ya gane ta a yanzu kamar yadda ya santa a baya.

Wannan magana tasa, hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala, ya ce da El-Rufai yana cikin gwamnati, da zai soki APC ba.

Sai dai tsohon gwamnan ya musanta hakan, yana mai cewa zai ci gaba da fadin gaskiya, ko yana da mukami ko babu.

El-Rufai ya fadi alhinin halinsa a siyasa

"Ina godiya da wadannan kalamai naka masu dadi @irahabib.
“Gaskiya, ba na iya yin munafurci, kasancewa kamar dan wasan kwaikwayo a gwamnati na wasu ne, ba na irinmu ba."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya musanta neman muƙami a wurin Tinubu

Kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta ikirarin neman mukami a gwamnatin Bola Tinubu, yana mai cewa ya riga ya bayyana matsayinsa.

Kara karanta wannan

"Gwamnatinmu ba za ta raga ba," Abba Gida Gida ya zare takobin yaki da rashawa

El-Rufai ya zargi wasu masu kare gwamnatin Tinubu da fifita bukatunsu akan gaskiya, yana mai cewa biyayya ga Allah da kasa ta fi kowanne muhimmanci.

Tsohon gwamnan ya ce ko da kuwa yana cikin gwamnatin Bola Tinubu zai caccake tsarinsa idan ya ga abin da bai dace ba kamar yadda ya ce ya yi a da.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel