Kaduna: Gwamna Ya Ba Tsohon Dan Majalisa Mukami, Ya ba Wasu 2 Kujeru a Gwamnati
- Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya nada Hon. Ado Dogo Audu, tsohon dan majalisar tarayya a matsayin mai ba da shawara kan harkokin siyasa
- Gwmanan ya kuma nada Abubakar Shehu Giwa da Ahmad Shehu Haruna a matsayin masu ba da shawara na siyasa da kuma tattalin arziki
- Mai girma Sanata Uba Sani ya bukaci wadanda aka ba mukaman su taimaka wajen kyautata mulki da karfafa hulda da jama’an Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi sababbin nade-nade a gwamnatinsa domin inganta muki.
Gwamna Uba Sani ya nada tsohon dan Majalisar Wakilai, Hon. Ado Dogo Audu, a matsayin mai ba da shawara kan harkokin siyasa.

Asali: Twitter
Gwamna Uba Sani ya yi sababbin nade-nade
Leadership ta ce gwamnan ya kuma nada Abubakar Shehu Giwa a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai kuma Ahmad Shehu Haruna da aka nada a matsayin mai ba da shawara kan harkokin tattalin arziki a jihar.
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan, Ibraheem Musa shi ya tabbatar da haka a ranar Juma’a 31 ga watan Janairun 2025.
Musa ya ce an yi wadannan nade-nade ne domin kawo sabbin ra’ayoyi a cikin gwamnatin jihar tare da ingata shugabanci.
Ya ce nadin zai taimaka wajen inganta ayyukan gwamnati tare da karfafa hulda da ‘yan jihar Kaduna domin samun ci gaba mai dorewa.
Gwamna ya shawarci sababbin hadimansa a Kaduna
Musa ya kara da cewa nade-naden za su fara aiki nan take, kuma gwamna Uba Sani ya umarce su da su hada kai domin tsara da aiwatar da sabbin shirye-shirye.
“Gwamnan ya bukace su da su hada kai domin bullo da sababbin tsare-tsare da shirye-shirye da za su karfafa hulda tsakanin gwamnati da jama’a tare da inganta ayyuka."

Kara karanta wannan
El Rufa'i ya kara girgiza siyasar Najeriya bayan ganawa da 'yan jam'iyyar SDP a Abuja
- Cewar sanarwar
Ta'addanci: Gwamnan Kaduna ya magantu kan sulhu
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa shawarar sulhu da ‘yan ta’adda ta biyo bayan koke ne da roƙon al’ummar da hare-haren suka fi shafa.
Ya ce ba a biya ko sisi ba don samun sulhu, yana mai cewa an cimma yarjejeniyar bayan ‘yan ta’adda sun saki mutum 200.
Gwamna Sani ya fadi abin da ya ke son cimma wa a Kaduna bayan shiga yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan ta'addan jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng