Abin na Manya ne: Yan Majalisa Sun Barke da Zanga Zanga a Abuja, Sun Jero Bukatu

Abin na Manya ne: Yan Majalisa Sun Barke da Zanga Zanga a Abuja, Sun Jero Bukatu

  • ‘Yan majalisar Zamfara guda 10 da aka dakatar sun yi zanga-zanga a Abuja, suna cewa hakan barazana ce ga dimukuradiyya.
  • Dakatattun yan majalisar sun ce amincewa da kasafin kudin 2025 da mambobin suka yi ba bisa doka ba ne, kuma sun shigar da korafi a Abuja
  • Wasu sun bukaci a janye dakatarwarsu tare da mayar da kujerar Shugaban ‘Yan Adawa Aliyu Ango Kagara da suka ce an soke ba bisa ka’ida ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Wasu daga cikin ‘yan majalisar dokoki a jihar Zamfara da aka dakatar sun gudanar da zanga-zanga a birnin tarayya watau Abuja.

Dakatattun yan majalisar sun gudanar da zanga-zangar a yau Juma’a 31 ga watan Janairun 2025 suna masu cewa dakatar da su barazana ce ga dimukuradiyya.

Kara karanta wannan

Tankar fetur ta yi bindiga a gidan mai a Jigawa, ta tayar da gobara

Yan majalisar Zamfaera da aka dakatar sun yi zanga-zanga
Dakatattun yan majalisar Zamfara guda 10 sun barke da zanga-zanga a Abuja. Hoto: Legit.
Asali: Original

Dakatattun yan majalisa sun yi zanga-zanga

Daily Trust ta ruwaito cewa yan siyasar sun bukaci yi musu adalci kan matakin da majalisar ta dauka kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Ibrahim Tudu Tuku, wanda ya karanta takarda da ya rattaba hannu tare da sauran ‘yan majalisa tara, ya ce yawancin shawarar da saura ‘yan majalisa 14 suka dauka da amincewa da kasafin kudin 2025, ba bisa ka’ida ba ne.

‘Yan majalisar da suka fusata, sun hada da yan jam'iyyar PDP mai mulkin jihar guda shida da hudu daga APC.

Yan siyasar sun shigar da korafi

Sun ce sun shigar da korafi ga Majalisar Tarayya, suna fatan za a warware matsalar, amma har yanzu ba a dauki mataki ba.

Haka kuma sun bayyana cewa ayyana kujerar Shugaban marasa rinjaye Aliyu Ango Kagara a matsayin wacce babu kowa a kanta ba bisa doka ba ne.

“Mun kasance a karkashin dakatarwa ba bisa ka’ida ba daga Majalisar saboda kawai mun ki bin umarnin su da zama tamkar yan amshin shata ga bangaren zartarwa.

Kara karanta wannan

"Daga Amurka aka samo kudin," Dattijo ya tona yadda aka nemi hana Tinubu takara

“Muna kira da a gaggauta soke ayyana kujerar Shugaban marasa rinjaye da ke wakiltar Talata-Mafara ta Kudu, Hon. Aliyu Ango Kagara a matsayin wanda babu kowa a kanta.
“Mun shigar da korafi zuwa Majalisar Dokoki ta Kasa, sun kira mu, suka ce mu koma gida, za su gayyace mu don bincike amma har yanzu ba mu ji komai daga gare su ba."

- Cewar yan majalisar

Wadanda dakatarwar ta shafa a Zamfara

Daga cikin wadanda abin ya shafa akwai Hon. Faruk Musa Dosara (Bakura), Hon. Shamsudeen Hassan, Hon. Bashar Aliyu (Talata-Mafara ta Arewa), Hon. Nasiru Abdullahi (Maru), da Hon. Barr. Bashir Abubakar Masama (Mara Arewa).

Sauran su ne Hon. Amiru Ahmed, Hon. Basiru Bello (Tsafe ta Yamma), Hon. Aliyu Ango Kagara (Talata-Mafaa Kudu), da Hon. Mukhtaru Nasiru (Kaura Namoda ta Arewa).

Majalisa ta tsige mambanta a Zamfara

Kun ji cewa Majalisar dokokin Zamfara ta tsige Hon. Aliyu Kagara tare da ayyana kujerarsa a matsayin wanda babu kowa a kai, bisa dogaro da sashe na 101 da 109(2) na kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Majalisar dokokin Kano ta fusata bayan gano abin da ake yi a gidajen da Kwankwaso ya gina

Duk da kafa kwamitoci da dama don tattaunawa da Hon. Aliyu Kagara, ba a samu damar yin sulhu ba, lamarin da ya kai ga yanke wannan hukunci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel