Gwamnonin PDP 12 Sun Shiga Ganawar Sirri yayin da Rikicinta Ke Neman Ɗaiɗaita Ta

Gwamnonin PDP 12 Sun Shiga Ganawar Sirri yayin da Rikicinta Ke Neman Ɗaiɗaita Ta

  • Yayin da jam'iyyar PDP ke ci gaba da fuskantar matsalolin cikin gida, gwamnoninta a Najeriya sun shiga wata ganawa
  • Gwamnonin jam'iyyar guda 12 suna wata ganawa a asirce a Asaba, babban birnin Jihar Delta, domin tattauna wasu batutuwa
  • An samu labari cewa wannan taro ba shi da alaka da rikicin jam'iyyar, kuma gwamnonin sun isa gidan gwamnati tun daren Alhamis
  • 'Yan jarida sun cika harabar dakin taron suna jiran sakamakon ganawar a gidan gwamnati, domin jin abubuwan da suka tattauna a zaman

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Asaba, Delta - Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya sun shiga wata ganawar sirri.

An tabbatar cewa gwamnonin guda 12 suna ganawa a asirce a Asaba, babban birnin Jihar Delta.

Gwamnonin PDP suna ganawar sirri a Delta
Gwamnonin PDP suna wata ganawar sirri a Delta yayin da jam'iyyar ke cikin rigima. Hoto: PDP Governors' Forum.
Asali: Facebook

Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun fara taɓa manya, an yi garkuwa da shugaban hukumar zaɓe ta jiha

Punch ta ruwaito cewa ana gudanar da taron ne a cikin sirri ba tare da sanin cikakken musabbabin ganawar tasu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya biyo bayan matakin gwamnonin jam’iyyar PDP na kiran taron gaggawa a Asaba, Delta, domin tattauna matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar tun bayan zaɓen 2023.

Taronsu na BoT da aka gudanar a Abuja ya rikide zuwa cacar baki bayan magoya bayan Sanata Samuel Anyanwu sun kai wa Sunday Ude-Okoye hari.

Shugaban jam’iyyar na rikon kwarya, Umar Damagum, ya bayyana cewa shugabanninsu ne ke ƙara ruruta rikicin da ke neman tarwatsa PDP mai adawa.

Abin da gwamnonin PDP suka tattauna

Shafin PDP Governor's Forum ya wallafa a Facebook abubuwan da suka tattauna ciki har da ci gaban da gwamnonin jam'iyyar suka kawo a Najeriya.

Sai kuma matsaloli da rigingimun jam'iyyar da halin kunci da gwamnatin Bola Tinubu ta jefa al'umma a ciki.

Kara karanta wannan

Gwamoni sun kira taron gaggawa bayan an ba hamata iska a taron PDP

Har ila yau, gwamnonin sun kara wa yan Najeriya karfin guiwa kan kokarinta domin dawo wa kan karagar mulkin kasar.

Gwamnonin PDP suna ganawar sirri a Delta

Wasu majiyoyi suna cewa wannan taro ba shi da alaka da rikicin jam'iyyar da ya yi katutu wanda ke neman ɗaiɗaita ta.

Gwamnonin sun isa gidan gwamnatin jihar Delta tun a daren jiya Alhamis 30 ga watan Janairun 2025.

Kuma an ce tun a daren jiya suke tattaunawa kan wasu batutuwa da ba a tabbatar da su amma suna da matukar muhimmanci.

'Yan jarida suna jiran sakamakon taron a harabar gidan gwamnati da fatan jin abubuwan da suka tattauna a wannan zama.

Atiku bai halarci taron kusoshin PDP ba

Kun ji cewa Atiku Abubakar bai halarci taron PDP na Arewa maso Gabas ba, bai kuma aika wakili ko bayar da hakuri kan rashin zuwansa ba.

Shugaban riko na PDP, Umar Ilya Damagum ya bukaci kusoshin da su daina rikici da junansu wanda ke kawo rarrabuwar kai da neman tarwatsa jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Abincin wasu ya kare: Gwamna ya fatattaki kwamishinoni 5, an maye gurbinsu nan take

A wajen wannan taro, PDP ta yanke shawarar sauya shugabanci a jihohi, tare da kokarin dawo da tsofaffin shugabanni cikin jam’iyyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel