El Rufa'i Ya Kara Girgiza Siyasar Najeriya bayan Ganawa da 'yan Jam'iyyar SDP a Abuja

El Rufa'i Ya Kara Girgiza Siyasar Najeriya bayan Ganawa da 'yan Jam'iyyar SDP a Abuja

  • Taron da shugaban SDP ya dauki hankali, Nasir El-Rufai, Ahmad Babba Kaita, da Mustapha Inuwa sun tattauna kan makomar Najeriya
  • Shugaban jam’iyyar, Shehu Musa Gabam, ya ce SDP na shirin sake fasalin siyasar kasar, tare da kawo kawo sauye sauye a Najeriya
  • Masu ruwa da tsaki a siyasa da magoya baya sun fara tofa albarkacin bakinsu kan sabon yunkurin SDP da suka shafi siyasar kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A yayin da rikicin siyasa ke kara kamari a Najeriya, jam’iyyar SDP ta fara motsi mai karfi da ke tayar da hankalin manyan jam’iyyu.

A daren jiya ne wasu fitattun ‘yan siyasa suka hallara a hedikwatar SDP, domin tattaunawa kan makomar kasar nan da kuma hanyar da za a bi domin ceto talakawa daga halin da suke ciki.

Kara karanta wannan

Abin da shugaban BoT ya faɗa a wurin taron PDP bayan an mari babban jigo a Abuja

Taron SDP
El-Rufa'i da 'yan siyasa sun gana da shugabannin SDP. Hoto: Shehu Musa Gabam ,SDP National Chairman
Asali: Facebook

Shugaban SDP na kasa, Shehu Musa Gabam ya wallafa a Facebook cewa jam'iyyar na shirin kawo sauyi a siyasar kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya samu halartar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, Sanata Ahmad Babba Kaita, da kuma tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Inuwa.

Shugaban SDP na kasa, Shehu Musa Gabam, ya ce yunkurin ba wai taron siyasa ne kawai ba, wata gagarumar hanya ce da ke neman sauya alkiblar siyasar Najeriya gaba daya.

Gabam ya fadi sabuwar alkiblar SDP

A yayin taron, shugabannin SDP sun bayyana cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen jagorancin jam’iyyun siyasa da suka shafe shekaru suna mulki ba tare da cika alkawuran da suka dauka ba.

Malam Nasir El-Rufai da sauran shugabanni sun amince cewa akwai bukatar samar da sabuwar hanya da za ta bai wa ‘yan Najeriya damar cin moriyar dimokuradiyya da gaske.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

A cewar Shehu Musa Gabam:

"Muna kokarin sake fasalin siyasar Najeriya, kuma mun fara da Katsina. Al’umma sun gaji, sun kosa, kuma iskar sauyi na kadawa fiye da kowane lokaci."

Wannan jawabi na nuna cewa SDP na shirin karbe madafun iko daga hannun jam’iyyun da suka dade suna rike da shugabanci a kasar, musamman APC da PDP.

Ra’ayoyin al’umma kan taron

Bayan wannan taro, magoya bayan jam’iyyar SDP da masu ruwa da tsaki a harkar siyasa da 'yan kasa sun fara bayyana ra’ayoyinsu kan lamarin.

Nuhu Abdullahi Sada ya ce:

"Taron yana samun gagarumin karbuwa! Tare da shahararrun mutane irin su El-Rufai, Sanata Ahmad Babba Kaita, da Mustapha Inuwa,
"Hakan ya bayyana karara cewa SDP na shirin sauya alkiblar siyasar Najeriya. Kiraye-kirayen sauyi daga talakawa na kara karfi, kuma SDP ce ke jagorantar wannan canji."

Kwamared Isa Saidu Kwankwaso ya ce:

Kara karanta wannan

Jerin ma'aikatun da wuraren da aka sanya wa sunan Bola Tinubu bayan hawansa mulki

"Barka da kokari, jagoran SDP na kasa, Alhaji Shehu Musa Gabam. Muna godiya matuka da irin kokarin da kake yi don ceton talakawan Najeriya daga halin da muke ciki."

Amin Hassan El-Yaqub ya ce:

"Ku ci gaba da aiki tukuru! Muna goyon bayan ku. Wadannan shugabanni marasa kishin kasa su koma inda suka fito a 2023. Ya isa haka!"

PDP za ta yi taron gaggawa a Delta

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta shirya taro a jihar Delta inda za ta tattauna muhimman abubuwa da suka shafi siyasa.

Rahotanni sun nuna cewa za a gudanar da taron ne a ranar Juma'a domin shawo kan matsalolin da suka addabi jam'iyyar, musamman bayan taron da ta yi a Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel