Gwamoni Sun Kira Taron Gaggawa bayan an ba Hamata Iska a Taron PDP

Gwamoni Sun Kira Taron Gaggawa bayan an ba Hamata Iska a Taron PDP

  • Gwamnonin jam’iyyar PDP sun shirya taron gaggawa a Asaba, Delta, domin tattauna matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar tun bayan zaɓen 2023
  • Taronsu na BoT da aka gudanar a Abuja ya rikide zuwa cacar baki bayan magoya bayan Sanata Samuel Anyanwu sun kai wa Sunday Ude-Okoye hari
  • Shugaban jam’iyyar na rikon kwarya, Umar Damagum, ya bayyana cewa shugabanninsu ne ke ƙara ruruta rikicin da ke neman tarwatsa PDP mai adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar adawa ta PDP na ci gaba da fama da rikice-rikice tun bayan zaɓen 2023, lamarin da ya jawo hankulan gwamnoninta da sauran shugabanni.

A ranar Laraba, yayin taron kwamitin amintattu na jam’iyyar (BoT) da aka gudanar a Abuja, an samu hargitsi bayan magoya bayan Sanata Samuel Anyanwu sun farmaki Sunday Ude-Okoye.

Kara karanta wannan

Abin da shugaban BoT ya faɗa a wurin taron PDP bayan an mari babban jigo a Abuja

Gwamnonin PDP
Gwamnonin PDP za su yi taro a Delta. Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Twitter

Punch ta wallafa cewa lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce, wasu jiga-jigan jam’iyyar suka nuna rashin jin daɗinsu da yadda abubuwa ke faruwa a PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa

A ƙoƙarin shawo kan matsalolin da suka addabi jam’iyyar, gwamnonin PDP sun shirya taron gaggawa da za a gudanar a ranar Juma’a a Asaba, Delta.

An ruwaito cewa gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ne zai jagoranci taron kuma zai tattauna batutuwa kamar:

  • Buƙatar gudanar da taron kwamitin gudanarwa na ƙasa (NEC)
  • Shirin gudanar da tarukan mazabu da jihohi
  • Rikicin da ya shafi Sakatare na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu
  • Rahoton shugaba Umar Damagum kan halin da jam’iyyar ke ciki
  • Matsalar shugabanci da ke ci gaba da ruruwa a PDP

A cewar wani jigo a jam’iyyar, akwai matsaloli da ke buƙatar a warware su cikin gaggawa kafin PDP ta rasa nagartarta a idon al’umma.

Kara karanta wannan

NNPP ta roki tsohon gwamna ya dawo gare ta bayan barin APC, ta yi misali da Abba Kabir

Maganar Damagum kan rikicin jam'iyyar PDP

Shugaban jam’iyyar na rikon kwarya, Umar Damagum, ya bayyana cewa shugabannin PDP ne ke ruruta rikicin da ke neman tarwatsa jam’iyyar.

A cewarsa:

"Wasu shugabanninmu da ya kamata su haɗa kan jam’iyya, su ne ke haddasa rikici da ƙirƙirar rabuwar kai."

Ya kuma yi gargadi da cewa, idan har PDP ta cigaba da tafiya a haka, za ta ci gaba da fuskantar matsaloli a gaba.

Martanin APC kan rikicin cikin gidan PDP

Jam’iyyar APC ta mayar da martani kan rikicin da PDP ke fuskanta, inda ta ce hakan yana nuna ƙarancin tsarin shugabanci a cikinta.

Shugaban sashen yaɗa labaran APC, Bala Ibrahim, ya ce:

"PDP ba ta da wani tsari na shugabanci. Abin da ke faruwa a cikinta yana nuna cewa Allah ne ya ceci Najeriya daga hannunta bayan mulkin shekarun 16.

Kara karanta wannan

"An mari babban jigo," Jami'an tsaro sun mamaye hedkwatar PDP ta ƙasa a Abuja

"A yanzu, jam’iyyar ta zama abin dariya."

Ya kuma bayyana cewa idan PDP na so ta koyi yadda ake tafiyar da siyasa, sai ta je makarantar siyasar APC da aka kafa ƙarƙashin jagorancin Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje.

APC ta kori tsohon ministan Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta kori tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, Rauf Aregbesola daga tafiyarta.

Rahotanni sun nuna cewa jam'iyyar APC ta kori Rauf Aregbesola ne kan wasu zarge zarge da suka hada da cin amanar jam'iyya da sauransu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel