Ta Faru Ta Kare: APC Ta Kori Tsohon Ministan Buhari daga Jam'iyya

Ta Faru Ta Kare: APC Ta Kori Tsohon Ministan Buhari daga Jam'iyya

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Osun ta ɗauki matakin ladabtarwa a kan tsohon ministan harkokon cikin gida, Rauf Aregbesola
  • APC ta kori tsohon gwamnan na jihar Osun bisa zargin cin dunduniyarta da kuma wasu zarge-zarge da ake yi masa
  • Kwamitin gudanarwa na APC na Osun ya ce an ɗauki matakin korar Aregbesola ne bayan samun rahoto kan binciken da aka yi a kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Osun - Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta kori tsohon ministan harkokin cikin gida a gwamnatin Muhammadu Buhari, Rauf Aregbesola.

Jam'iyyar APC ta kori tsohon ministan harkokin cikin gidan ne bisa zargin aikata laifin cin amanarta.

APC ta kori Aregbesola
Jam'iyyar APC ta kori Aregbesola Hoto: RAUF AREGBESOLA
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da kwamitin gudanarwa na APC na jihar Osun ya fitar.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka kori tsohon ministan Buhari daga APC?

Takardar dai an fitar da ita ne domin sanar da tsohon gwamnan na jihar Osun, matakin da kwamitin ya ɗauka na korarsa daga jam'iyyar APC, rahoton The Punch ya tabbatar.

"Bayan kammala bincike, kwamitin gudanarwa na jiha (SEC) ya yi nazari kan rahoton kwamitin ladabtarwa."
"Bayan yin nazari sosai kan sakamakon bincike da shawarwarin kwamitin, SEC ya yanke shawarar amincewa da korarka nan take daga jam'iyyar APC."
"Wannan matakin ya dogara ne da hujjojin da ke tabbatar da ayyukanka da suka tarwatsa haɗin kai da ƙimar jam’iyya, wanda ya saɓa da tanadin sashe na 21 na kundin tsarin mulkin APC."
“Sakamakon haka, bisa amincewa da korarka, ka daina kasancewa mamba na APC. Haka kuma, ba za ka sake wakiltar jam’iyyar a kowane matsayi ba ko kuma ka riƙa ɗaukar kanka a matsayin mamba na jam’iyya."

- Kwamitin SEC

Duk da haka, jam’iyyar APC ta yabawa Aregbesola bisa gudunmawar da ya bayar a baya ga jam’iyyar, tare da jawo hankalinsa kan ya mutunta hukuncin korarsa daga APC.

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko Radda ya yi bayani bayan 'mika' mulkin Katsina ga PDP

Rauf Aregbesola ya tuburewa APC

Rauf Aregbesola, wanda ya yi gwamna na tsawon shekaru takwas a Osun, ya kafa ƙungiyar siyasa a cikin APC da aka sani da The Osun Progressives (TOP), wacce aka sake mata suna zuwa Omoluabi.

An zargi ƙungiyar da taka rawa wajen jefa APC cikin rashin nasara a zaɓen gwamnan jihar Osun na 2022.

A ranar Lahadi, ƙungiyar Omoluabi, ƙarƙashin jagorancin Aregbesola, ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar APC, tana mai cewa farin jinin jam’iyyar ƙare a jihar.

Jam'iyyar APC ta caccaki ƙungiyar Omoluabi

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Osun ta caccaki ƙungiyar Omoluabi wacce ta sanar da ficewarta daga jam'iyyar.

APC ta bayyana cewa ƙungiyar ta yi kuskure domin ta kama hanyar da za a manta da ita a tarihin siyasa sakamakon ficewarta daga jam'iyyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel