'Babu Ministan Tinubu da Ya Fi Shi': Jigon APC Ya Kare El Rufai, Ya Hango Kuskuren Jam'iyya
- Jigon APC, Joe Igbokwe ya bukaci APC ta daidaita da Nasir El-Rufai, yana cewa babu Minista a gwamnati da ya fi shi basira ko jarumta
- Igbokwe ya gargaɗi APC kada ta bar El-Rufai ya koma jam’iyyar adawa, yana jaddada irin gudunmawar da ya bayar a lokacin zaɓen 2023
- Hakan ya biyo bayan martanin APC ga El-Rufai, inda kakakinta Felix Morka ya zarge shi da rashin kwarewa bayan da ya soki jam’iyyar mai mulki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar APC a Lagos, Joe Igbokwe, ya bukaci jam’iyyar da ta daidaita da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
Igbokwe ya ce babu wani Minista a cikin gwamnatin Bola Tinubu da ya fi El-Rufai wayau ko ƙarfin hali wajen gudanar da mulki.

Asali: Twitter
El-Rufai ya caccaki salon mulkin Bola Tinubu
Igbokwe ya faɗi haka a shafinsa na Facebook bayan da El-Rufai ya zargi APC da yunƙurin rushe jam’iyyun adawa a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana hakan ne a wani taro da Cibiyar Jagoranci, Dabaru da Ci Gaban Afirka ta shirya a Abuja.
El-Rufai ya ce APC ta kauce wa manufofinta na farko kuma dole ne a dawo da martabar siyasar Najeriya.
“Akwai alamar wani shiri na musamman domin tarwatsa jam’iyyun adawa."
- Nasir El-Rufai
Jigon APC ya gargadi jam'iyyar kan taba El-Rufai
Duk da haka, Igbokwe ya ja hankalin APC cewa ba za ta iya barin El-Rufai ya koma jam’iyyar adawa ba.
“APC na buƙatar Malam Nasir El-Rufai saboda irin kokarin da ya yi wajen tallafa wa jam’iyya a zaɓen 2023."
“An naɗa shi Minista, amma wasu mutane marasa mutunci sun hana shi samun wannan mukami ba tare da dalili ba."
“Ba za mu bar wannan mutum mai hazaka ya tafi jam’iyyar adawa ba. APC na bukatar El-Rufai fiye da kowane lokaci, duk da irin kwarewarsa, an bar El-Rufai a gefe. Ina so in tambaya, wane minista ne ya fi shi basira da ƙwarewa?"
- Joe Igbokwe
Dan APC ya fadi gudunmawar El-Rufai ga jam'iyyar
Kusa a jam'iyyar APC ya tuna irin ƙoƙarin da tsohon gwamnan ya yi don ganin APC ta ci gaba da mulki a Kaduna, duk da matsalolin kuɗi.
A cewarsa, kin bai wa El-Rufai damar aiki a gwamnatin APC babban kuskure ne da bai kamata a yi ba.
Hadimin Tinubu ya yi martani ga El-Rufai
Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya yi gargadi kan barazanar da dimokuradiyya ke fuskanta a Najeriya.
Biyo bayan kalaman tsohon gwamnan, hadimin shugaba Tinubu, Daniel Bwala, ya mayar da martani ga kalaman El-Rufa’i.
Nasir El-Rufa’i ya zargi APC da rasa alkibla tare da bayyana matsalolin shugabanci da kaucewa tsarin asali da aka gina ta a kai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng