"An Mari Babban Jigo," Jami'an Tsaro Sun Mamaye Hedkwatar PDP Ta Ƙasa a Abuja

"An Mari Babban Jigo," Jami'an Tsaro Sun Mamaye Hedkwatar PDP Ta Ƙasa a Abuja

  • Jami'an tsaro da suka kunshi sojoji da ƴan sanda sun kai ɗauki babbar hedkwatar PDP ta ƙasa da ke Abuja bayan rigima ta ɓarke a taron BoT
  • Rahotanni sun nuna cewa rigimar ta ɓarke ne lokacin da Samuel Anyanwu da Ude-Okeye suka dura wurin taron, lamarin da ya kai ga marin ɗayansu
  • Majalisar amintattu ta PDP watau BoT ta shirya taron ne domin tattaunawa kan rikicin PDP wanda ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa tun bayan zaɓen 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Jami'an tsaro sun mamaye babbar sakatariyar jam'iyyar PDP ta ƙasa da ke Wadata Plaza a babban birnin tarayya Abuja.

Dakarun hukumomin tsaron sun yi wa sakatariyar kawanya ne sakamakon rigimar da ta ɓarke a wurin taron ƴan Majalisar amintattun PDP watau BoT.

Kara karanta wannan

Manyan ƙusoshi 2 sun yi arangama a wurin taron majalisar amintattun PDP a Abuja

Jami'an tsaro.
Jami'an tsaro sun kai ɗauki hedkwatar PDP da rigima ta kaure a Abuja Hoto: Abdulrahman Zakariyau
Asali: Facebook

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa Sanata Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoyes sun yi arangama a wurin taron, hakan ya sa jami'an tsaro kai ɗauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rigima ta ɓarke a hedkwatar PDP

Manyan ƙusoshin guda biyu dai sun jima suna rigima kan kujerar sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa.

An ruwaito cewa rikicin ya ɓarke ne a lokacin da Anyanwu da Ude-Okoye suka isa wurin taron BoT kowane a matsatin sakataren jam'iyyar PDP.

Wani hadimi ga Samuel Anyanwu ne ya kori Ude-Okoye daga ɗakin taron da karfin tsiya jim kadan bayan shiga wata ganawar sirri.

Lamarin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce mai zafi tsakanin ɓangarorin guda biyu kafin jami’an tsaro su shiga tsakani.

Dakarun tsaron da aka gani sun kai ɗauki sakatariyar PDP sun haɗa da sojoji, ƴan sanda da kuma jami'an hukumar tsaro da NSCDC.

Hadimin Anyanwu ya mari babban jigo

A rahoton The Nation, Emmanuel Okoronkwo, mataimaki ga Anyanwu, wanda a baya ya ci zarafin wani dan jarida a sakatariyar PDP, ya ɗaga hannu ya mari Udeh-Okoye.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta

Bayan haka kuma an ce ya haɗa kai da wasu magoya bayan Sanata Anyanwu, suka fitar da Ude-Okoye daga wurin taron da ƙarfin tsiya.

Da farko dai jami'an tsaro sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen shawo kan hargitsin amma daga bisani faɗan ya sake dawowa ɗanye.

Jami'an tsaro sun kai ɗauki wurin taron BoT

Rigimar ta sake barkewa ne mintuna 10 bayan komai ya lafa, inda Udeh-Okoye ya koma wurin taron tare da mutane kusan goma sanye da bakaken kaya. 

An ga dakarun ‘yan sanda da babban jami’in tsaro na jam’iyyar PDP suna rokonsa da ya sassauta lamarin, ya kwantar ɗa hankalinsa.

Sama da magoya baya 50 daga kowane bangare ne suka hallara a wajen sakatariyar jam’iyyar PDP a halin yanzu.

Jigo ya bankaɗo tushen rikicin PDP

A wani labarin, kun ji cewa Dele Momodu ya bayyana cewa rikicin PDP ta fara ne tun daga zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban kasa a shekarar 2022.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga Kano, sun sace diyar babban attajirin dan kasuwa

Bsbban jigon ya ce rashin nasarar tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ministan Abuja na yanzu ne tushen matsalar PDP, ya kuma zargi PDP da rura wutar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel