Manyan Ƙusoshi 2 Sun Yi Arangama a Wurin Taron Majalisar Amintattun PDP a Abuja
- Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye sun yi arangama yayin taron Majalisar Amintattu (BoT) ta jam’iyyar PDP kan kujerar sakatare na kasa
- A ranar 20 ga Disamba, 2024, kotun ɗaukaka ƙara a Enugu ta tabbatar da Ude-Okoye a matsayin halastaccen sakataren PDP, bayan Anyanwu ya yi takara
- Bayan rasa kujerarsa, Anyanwu ya shigar da buƙatar dakatar da hukuncin kotu, tare da ɗaukaka ƙara, lamarin da ya ƙara dagula rikicin cikin PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - An ɗan samu hatsaniya kafin fara taron Majalisar amintattun PDP (BoT) ta ƙasa a babban brinin tarayya Abuja ranar Laraba, 29 ga watan Janairu, 2025.
Rahotanni sun nuna cewa hatsaniyar ta faru ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye, waɗanda ke rigima kan kujerar sakataren PDP na ƙasa.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa manyan jiga-jigan biyu sun yi arangama da juna gabanin fara taron BoT yau Laraba a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba ku manta ba babbar jam'iyyar adawa ta kasa watau PDP na fuskantar rikice-rikicen cikin gida a ɓangarori daban-daban.
Kan haka ne Majalisar amintattu watau BoT ta shirya zama don tattaunawa game da batutuwan da suka shafi PDP.
Kusoshin PDP sun yi arangama a taron BoT
Bayanai sun nuna cewa Sunday Ude-Okoye ya isa dakin taron kafin isowar Anyanwu da Ambasada Umar Iliya Damagum, wanda ke rikon kujerar shugaban PDP na ƙasa.
Sai dai, bayan Anyanwu ya iso, take aka tilasta wa Ude-Okoye barin dakin taron, amma daga baya ya koma bayan wasu daga cikin magoya bayansa da ke cikin BoT sun iso.
Rigima kan kujerar sakatare na ƙasa ta samo asali ne tun bayan da Anyanwu ya ajiye kujerarsa domin yin takarar gwamnan Imo, wanda ya sha kaye a hannun Gwamna Uzodinma.
Abin da ya jawo rigimar kujerar sakataren PDP
Tun farko da Anyanwu ya ajiye kujerar domin takarar gwamna, shugabannin PDP na Kudu maso Gabas suka zaɓi Ude-Okoye a matsayin wanda zai mare gurbinsa.

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta
Bayan Anyanwu ya sha ƙasa a zaben gwamnan Imo, yunƙurinsa na dawo wa da kujerar sakataren PDP na ƙasa ya ƙara jefa jam’iyyar cikin rikici.
A ranar 20 ga Disamba, 2024, kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Enugu ta tabbatar da hukuncin sauke Sanata Anyanwu daga matsayin sakataren PDP.
Haka nan kuma kotun ta tabbatar da Ude-Okoye a matsayin halastaccen mai rike da mukamin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Rigimar PDP ta kai gaban kotun koli
Duk da haka, Anyanwu ya shigar da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin tare da ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli.
Hakan ya ƙara dagula lamarin, musamman bayan da Damagum ya naɗa Dr. Musa (SAN) a matsayin lauyan jam’iyyar.
Yanzu haka ne dai ƴan BoT sun shiga taron da suka shirya a hedkwatar PDP ta ƙasa duk da rikicin da aka ɗan samu a farko.
Ƴan NWC 11 sun yi fito na fito da Damagum
A baya, kun ji cewa ƴan kwamitin gudanarwa watau NWC sun nuna adawa da matakin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum na naɗa lauyan jam'iyyar.
'Yan kwamitin su 11 sun bukaci kotun koli ta yi watsi da Dr. J. Y. Musa SAN da Damagum ya nada domin ya kare PDP a shari'ar kujerar sakatare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng