APC Ta Yi Martani bayan El Rufa'i Ya Kwance Mata Zani a Kasuwa

APC Ta Yi Martani bayan El Rufa'i Ya Kwance Mata Zani a Kasuwa

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai ya caccaki tsarin mulkin APC, yana mai cewa jam’iyyar ta lalace
  • Biyo bayan kalaman El-Rufa'i, fadar shugaban kasa da jam'iyyar sun yi martani da cewa tsohon gwamnan na neman bata wa APC suna
  • Sai dai jam’iyyun adawa sun marawa El-Rufai baya, suna cewa APC ta yi watsi da alkawuran da ta dauka a lokacin neman zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya caccaki jam’iyyar APC da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa mulkin jam’iyyar na cikin halin ha'ula'i.

Tsohon gwamnan ya ce APC ta wofintar da manufofinta na yaki da cin hanci, bunkasa tattalin arziki da kuma inganta tsaro.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

Tinubu El-Rufa'i
APC ta yi martani ga El-Rufa'i ka sukar jam'iyya. Hoto: Bayo Onanuga|Nasir El-Rufa'i
Asali: UGC

Punch ta wallafa cewa fadar shugaban kasa da jam’iyyar APC sun mayar da martani ga El-Rufai, suna cewa hakan zagon kasa ne da kuma bata wa jam’iyyar suna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Caccakar da Nasir El-Rufai ya yi wa APC

A wata tattaunawa kan karfafa dimokuradiyya a Abuja, El-Rufai ya bayyana cewa babu wata tsayayyar jam’iyya a kasar nan, yana mai cewa APC ba ta da cikakken tsari.

A cewarsa:

"Ba zan iya gane APC ba. Tun shekaru biyu da suka wuce, ba a taba yin wani taro na jam’iyya ba—ba taron shugabanni, babu NEC, babu komai.
"Na gaza gane ko jam’iyya ce ko kuma mulki ne na mutum daya, ko ma babu shugabanci kwata-kwata."

Ya kara da cewa yana da matukar muhimmanci a duba matsalar dimokuradiyya a cikin jam’iyyun siyasa, tare da kafa matakai masu inganci wajen zaben ’yan takara.

Martanin fadar shugaban kasa da APC

Kara karanta wannan

Bayan sukar APC, El Rufai ya yi magana kan shirinsa na barin jam'iyyar

Legit ta wallafa cewa fadar Shugaban kasa ta bayyana takaicinta kan kalaman El-Rufai, tana mai cewa tsohon gwamnan bai kyauta ba.

Daraktan yada labaran jam'iyyar APC, Bala Ibrahim, ya ce El-Rufai zai fi dacewa da ya kai korafinsa ga shugabancin jam’iyyar, maimakon fitowa fili yana sukar ta.

A cewar Bala Ibrahim;

"Dimokuradiyya tana bai wa kowa damar fadin albarkacin bakinsa. El-Rufai na da ’yancin fadin ra’ayinsa.
Amma ba lallai ne hakan na nufin gaskiya ba. APC na sauraron kowa, kuma idan yana da koke, ya san inda zai kai shi."

Ibrahim ya kara da cewa APC a karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje tana bai wa ’ya’yanta damar bayyana matsayarsu.

A karkashin haka Bala Ibrahim ya ce idan El-Rufai yana da wata matsala, zai iya tuntubar shugabannin jam'iyyar.

A yayin da APC ke kokarin kare kanta daga sukar El-Rufai, wasu jam’iyyun adawa sun goyi bayan ra’ayinsa, suna mai cewa APC ta kauce daga alkawurran da ta dauka ga 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

'Haba Malam': Hadimin Tinubu ya zargi El Rufa'i da neman rusa gwamnati kan sukar APC

APC: An dawo da maganar sauke Ganduje

A wani rahoton, kun ji cewa wasu manya a APC sun dawo da maganar sauke Abdullahi Ganduje daga shugabancin jam'iyya.

Hakan na zuwa ne yayin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba Ganduje matsayi a hukumar FAAN a makon da ya wuce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel