APC Ta Yi Kaca Kaca da Atiku Abubakar, Ta Fadi Wanda Ke Haddasa Rikici a PDP
- APC ta musanta zargin Atiku Abubakar na cewa gwamnatin Bola Tinubu ta bai wa jam’iyyun adawa cin hancin N50m
- Felix Morka ya ce Atiku da sauran jiga-jigan adawa ba su iya tafiyar da jam’iyyunsu, amma suna kokarin dora laifi kan APC
- APC ta zargi Atiku, Peter Obi da Nasir El-Rufai da kokarin neman mafita daga gazawarsu ta hanyar yi wa gwamnatin Tinubu sharri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Jam’iyyar APC ta caccaki Atiku Abubakar, kan zargin da ya yi na cewa gwamnatin Bola Tinubu ta bai wa jam’iyyun adawa cin hancin N50m.
Atiku ya yi wannan zargi ne a ranar Litinin yayin da yake jawabi a wani taron kasa da aka shirya kan karfafa dimokuradiyya a Abuja.

Asali: Twitter
Atiku ya zargi APC da ba da cin hancin N50m
Taron ya samu shirya wa ne daga cibiyoyin LS&D,CDD, da kungiyoyin WFD, PAACA, da NPC kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi gargadin cewa Najeriya na fuskantar barazanar rasa dimokuradiyyarta idan har aka ci gaba da tafiya a wannan hanya.
Legi Hausa ta rahoto Atiku yana cewa:
“Ina son bayyana wa jama’a cewa na hadu da shugabannin wata jam’iyyar adawa, inda suka amsa cewa wannan gwamnati tana ba su N50m."
Jam'iyyar APC ta yi martani ga zargin Atiku
Da yake mayar da martani, sakataren yada labaran APC, Felix Morka, ya ce zargin Atiku ba shi da tushe balle makama, kuma abin dariya ne.
A cewarsa, yayata jita-jita da yin zarge-zargen da ba su da tushe alamu ne na yanke kauna daga bangaren Atiku.
“Zargin Atiku na cewa gwamnatin APC na bai wa wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa N50m abu ne da ba shi da tushe kuma abin dariya.

Kara karanta wannan
'Haba Malam': Hadimin Tinubu ya zargi El Rufa'i da neman rusa gwamnati kan sukar APC
“Ya kamata a ce mutumin da ya taba zama mataimakin shugaban kasa bai tsaya kan irin wadannan zarge-zargen da ba su da asali ba."
- Felix Morka.
APC ta caccaki Atiku, Obi da El-Rufai
Kakakin APC ya kuma soki Atiku, Peter Obi da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kan zargin cewa APC na da hannu a rikicin jam’iyyun adawa.
Tashar Channels TV ta rahoto Felix Morka yana cewa:
“Zargin Atiku, Peter Obi da Nasir El-Rufai na cewa APC na haddasa rikici a cikin jam’iyyun adawa abin al'ajabi ne. Wannan dai kawai wata dabara ce ta boye gazawarsu.
“Ba su iya tafiyar da jam’iyyunsu yadda ya dace, amma suna da’awar cewa su ne za su iya mulkin kasa mafi yawan jama’a a Afirka.
“Ba za mu manta da yadda PDP ta yi amfani da karfi wajen kwace jihohin Kudu maso Yamma ba, tare da alkawarin mulki na tsawon shekaru 60.”
APC ta tuno da maganganun Obasanjo kan zabe
Morka ya ce a wancan lokacin ne tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa zabe abu ne da sai an yi nasara ko ta halin kaka.
"A lokacin da suke mulki, mai gidan Atiku, Cif Olusegun Obasanjo ya fito ya ce zabe abu ne da sai an yi nasara ko ta halin kaka, duk don su kwace Legas."
- Felix Morka.
Ya ce Najeriya ta cancanci samun siyasa mai ma’ana daga Atiku maimakon irin wadannan koke-koke marasa tushe da asali.
Atiku ya fadi matsalar dimokuradiyyar Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa Atiku Abubakar ya yi ikirarin cewa dimokuradiyya a Najeriya na cikin gagari saboda rashin tabbas a bangaren shari'a.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce bangaren shari'ar Najeriya ne ke kawo nakasu ga ci gaban dimokuradiyya wanda barazana ce da dole a dakile ta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng