"Ya Karya Doka," An Tsige Ɗan Majalisar APC daga Kujerarsa, INEC Za Ta Canza Zaɓe
- Hon. Aliyu Ango Kagara mai wakiltar Talata Mafara ya halarci zaman majalisar Zamfara sau 21 kawai daga cikin zama 180, wanda ya saba doka
- Majalisar dokokin ta tsige Kagara tare da ayyana kujerarsa a matsayin babu kowa, bisa dogaro da sashe na 101 da 109(2) na kundin tsarin mulki
- Duk da kafa kwamitoci da dama don tattaunawa da Hon. Aliyu Kagara, ba a samu damar yin sulhu ba, lamarin da ya kai ga yanke wannan hukunci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - Majalisar dokokin jihar Zamfara ta ayyana kujerar mambanta, Hon. Aliyu Ango Kagara, mai wakiltar mazabar Talata Mafara ta Kudu, a matsayin babu kowa.
Majalisar ta ce ta ɗauki wannan mataki na tsige ɗan majalisar ne saboda rashin halartar ayyukan da suka rataya a wuyansa na dogon lokaci.
Channels tv ta tattaro cewa ƴan Majalisar sun cimma wannan matsaya a zaman yau Talata, 28 Janairu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin tsige ɗan majalisar APC a Zamfara
Shugaban masu rinjaye, Hon. Bello Muhammad Mazawajje Tsafe ne ya gabatar da kudirin kuma mataimakin kakakin Majalisar, Hon. Adamu Aliyu Gummi, ya mara masa baya.
Wannan sanarwa ta fito ne ta hannun babban sakataren yada labarai na Majalisar dokokin jihar Zamfara, Bello Kurya.
Bello Kurya ya bayyana cewa Hon. Aliyu Kagara ya halarci zaman majalisar sau 21 ne kacal daga cikin zama 180 da Majalisar ta yi zuwa yanzu.
Ya ce hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin majalisar waɗanda suka tanadi cewa mambo su kasance suna halartar zama akai-akai.
Ƴan Majalisar da suka amince a tsige Kagara
A cewar sanarwar, ƴan Majalisar da suka goyi bayan tsige Aliyu Kagara sun haɗa da Hon. Kabiru Mikailu Dangulbi (Maru Kudu), da Hon. Rilwanu Marafa Nagambo Anka (Anka).
Sauran sun ƙunshi Hon. Ibrahim Garba Liman Fegin Mahe (Gusau II), da Hon. Adamu Aliyu Gummi (Gummi II).
Duk sun goyi bayan kudirin, suna mai jaddada mahimmancin tabbatar da da’a da martabar majalisar.
“Duk da haka, Hon. Halliru Abdullahi Kuturu (Zurmi Gabas) ya roƙi majalisar da ta yi amfani da wasu hanyoyi na ladabtarwa maimakon tsige ɗan majalisar," in ji sanarwar.
Majalisar Zamfara ta yi kokarin a sasanta
Sai dai kakakin Majalisar, Rt. Hon. Bilyaminu Ismail Moriki, ya sanar da tsige Aliyu Kagara tare da ayyana kujerarsa a matsayin wadda babu kowa.
Ya ce Majalisa ta cimma matsayar ne dogaro da sashe na 101 da 109(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya.
“Tun da farko, majalisar ta kafa kwamitoci da dama don tattaunawa da Hon. Aliyu Kagara, amma duk kokarin sulhu ya ci tura,” in ji sanarwar.
A halin yanzu hukumar zaɓe ta kasa watau INEC ta samu damar shirya zabon zaɓen cike gurbi a mazaɓar domin al'umma su sake zaɓen wanda zai wakilce su.
An tsige kakakin Majalisar dokokin Legas
Kuna da labarin cewa an tsige shugaban Majalisar dokokin jihar Legas, Hon. Mudashiru Obasa daga muƙaminsa bayan shekara da shekaru a ofis.
Ƴan Majalisar sun kuma zaɓi mace ta farko, Hon. Mojisola Meranda, mai wakiltar Apapa 1 a matsayin sabuwar shugabar Majalisar dokokin Legas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng