Wasu Yan Siyasa na Neman Canza Sunayen Talakawan da Za a ba Tallafin Kudi a Najeriya
- Ministan jin kai da rage talauci, Nentawe Yilwatda ya ce ma'aikatarsa za ta tabbatar da tallafin kuɗin da za a rabawa talakawa sun isa gare su
- Yilwatda ya ce akwai wasu ƴan siyasa da suka matsa masa lamba suna son a bar jihohi su zaɓi waɗanda za a ba wannan tallafi
- A cewarsa, haƙarsu ba za ta cimma ruwa da domin tsarin ba haƙa yake ba, ba na gwamnati ita kaɗai ba ce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ministan harkokin jinƙai da rage talauci, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa akwai wasu ‘yan siyasa da ke ƙoƙarin jirkita shirin tallafin kudin da za a yi
Ministan ya ce ƴan siyasar na yunƙurin tsoma hannu a rijistar sunayen waɗanda za su ci gajiyar shirin wanda gwamnatin tarayya ke tutawa magidanta tallafin kudi.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

Source: Twitter
Ministan ya bayyana haka ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan siyasa sun matsa lamba kan tallafi
A cewar Yilwatda, ma’aikatarsa tana fuskantar matsin lamba daga wasu masu ruwa da tsaki da ke so ta sassauta wasu tsare-tsare don cika buƙatunsu na siyasa.
Sai dai ya ce hakan ba zai yiwu ba saboda shirin ba na gwamnati ba ne ita kaɗai, haɗin gwiwa ne tsakanin ma’aikatar, bankin duniya, da ƙungiyoyin farar hula (CSOs).
Wannan, in ji shi, ya tabbatar da cewa aikin ba na ma’aikatar jin ƙai kadai ba ne, aiki ne na haɗin gwiwa wanda ke da tsari da dokoki masu inganci.
“Wasu suna son mu sassauta dokokin, mu bar gwamnoni ko jihohi kawai su samar da jerin sunayen wadanda za su amfana da shirin.
"Wannan shirin tallafin yana da sharuɗɗa masu ƙarfi waɗanda dole ne a bi kafin mutum ya cancanci amfana. Saboda haka, ba za mu bari wata alaƙar siyasa ta shafi wannan tsari ba,” in ji ministan.
Ministan ya ce ba ruwan talauci da siyasa
Yilwatda ya ƙara da cewa talauci ba ya bambanta mutane bisa la’akari da jam’iyyar siyasa, kabila ko yare.
“Talauci ba ya gane siyasa, ba ya gane kabila, sannan ba ya gane irin harshen da kake amfani da shi. Talaka dai talaka ne," in ji shi.
Don tabbatar da gaskiya da adalci, ministan ya bayyana cewa ma’aikatarsa ta dakatar da duk wata musayar kuɗi kai tsaye sannan ta mayar da hankali kan amfani da hanyoyin zamani.
Gwamnatin Bola Tinubu ta lissafa sharudɗa
Yanzu haka, ya ce ana buƙatar duk wanda zai amfana da shirin ya mallaki lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) da lambar tantancewa ta Banki (BVN) domin tabbatar da sahihanci.
Ministan ya ci gaba da cewa:
"Za mu tabbatar da gaskiya a tsarin rabon tallafin kudin nan ta hanyar amfani da ƙungiyoyi masu zaman kansu su bincka duk wasu bayanai da yadda aka turawa mutane kudin.
"Hakan zai taimaka mana wajen tabbatar da an gudanar da tsarin cikin gaskiya da rikon amana."

Kara karanta wannan
"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027
A ƙarshe, Yilwatda ya nuna cewa ma’aikatar tana aiki tukuru don tabbatar da cewa shirin tallafin kuɗi ya kai ga waɗanda suka cancanta ba tare da an sa siyasa ba.
Gwamnatin Tinubu za ta ɗauki matasa aiki
Kuna da labarin Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin mai girma Bola Tinubu ta bude shafin daukar matasa aiki a karkashin shirin kiwon lafiya na NHFP.
Gwamnatin ta sanar da cewa za ta biya waɗanda ta ɗauka alawus da kayan aiki domin inganta kiwon lafiya a yankunansu.
Asali: Legit.ng
