"A Shirye Nake Na Tuɓe Rigar Kariya, na Miƙa Kaina ga EFCC," Gwamna Ya Magantu

"A Shirye Nake Na Tuɓe Rigar Kariya, na Miƙa Kaina ga EFCC," Gwamna Ya Magantu

  • Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya yi magana kan abubuwan da ke faruwa a siyasar jiharsa a ƴan kwanakin nan
  • Da yake martani ga wata ƙungiya da ta nemi a sako EFCC da ICPC, Gwamna Eno ya ce a shirye yake ya tuɓe rigar kariya kuma ya miƙa kansa
  • Ya ce duk masu burin haɗa shi faɗa Bola Tinubu, Godswill Akpabio ko ubangidansa, Udom Emmanuel ba masoyan jihar Akwa Ibom ba ne

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya ce a shirye yake ya tube rigar kariyar da yake da ita kuma ya miƙa kansa ga hukumar yaƙi da rashawa (EFCC).

Gwamna Eno ya yi wannan furucin ne bayan wata kungiyar APC ta nemi EFCC da ICPC su binciki yadda aka kashe kuɗaɗen jama'a tun daga mulkin tsohon gwamna, Udon Emmenuel.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

Gwamna Umo Eno.
Gwamna Eno na jihar Akwa Ibom ya ce a shirye yake ya mika kansa ga EFCC Hoto: Umo Eno
Asali: Twitter

Umo Eno ya faɗi hakan ne a wata hira da manema labarai da ya yi kan abubuwan da ke faruwa a siyasar Akwa Ibom, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Na shirya miƙa kaina ga EFCC' - Gwamna Eno

Gwamma Umo Eno ya ce zai iya miƙa kansa ga EFCC ta yi duk binciken da za ta yi idan baƙatar hakan ta taso.

Da yake tsokaci kan abubuwan da ke faruwa ciki har da raɗe-raɗin shirin komawa APC, Gwamma Eno ya ce a yanzu ya maida hankali wajen gudanar da shugabanci.

Ya nuna damuwa kan masu yaɗa karya da kokarin ɓata duk wani jagoran siyasa a jihar Akwa Ibom.

Gwamna Eno ya faɗi waɗanda yake zargi

A cewar mai girma gwamnan, wasu bara-gurbi ne ke kirkiro maganganu mara tushe domin lalata alaƙarsa da shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Gwamna Umo Eno ya zarge su da yunƙurin haɗa shi faɗa da shugaban Majalisar dattawa, Godswill Akpabio da kuma uban gidansa na siyasa, Udom Emmanuel.

Kara karanta wannan

Wasu ƴan siyasa na neman canza sunayen talakawan da za a ba tallafin kudi a Najeriya

Tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, gwamnan ya tuna cewa ya samu nasarar kulla alaka mai kyau tsakaninsa da gwamnatin tarayya.

Gwamna Eno ya shawarci ƴan siyasa da sauran mazauna Akwa Ibom su daina zagin shugabanni saboda banbancin jam'iyyu.

"Shi (Akpabio) dan mu ne, kuma duk da bambancin jam’iyya, za mu ci gaba da ba shi goyon baya tare da kara masa kwarin gwiwar yi wa jihar Akwa Ibom hidima.”
"Na san akwai wasu jagorori da suke jin haushin shugaban majalisar dattawa, ko a jam'iyya ɗaya kuke wani lokacin za aka ga ba a shiri," in ji Eno.

Gwamna Eno yana mutunta Tinubu

Gwamnan ya sha alwashin cewa babu wani matsin lamba na siyasa da zai tursasa shi ya kama faɗa da shugaban Majalisar dattawa ba.

Ya kuma jaddada cewa yana matukar mutunta shugaba Bola Tinubu da minista Ekperiikpe Ekpo kuma a koda yaushe zai hada kai da su domin amfanin jihar.

Kara karanta wannan

"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

PDP ta ba Gwamnan Akwa Ibom tikiti

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta rufe ƙofar neman takarar gwamna a jihar Akwa Ibom, ta ce Gwamma Eno za ta ba tikitin a zaɓen 2027.

PDP ta ce ta zaɓi sake tsayar da gwamnan a karo na biyu tun yanzu ne saboda kyakkyawan shugabancin da ya kafa a jihar tun da ya ɗare kan madafun iko.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262