APC Ta Yi Tonon Silili bayan Tawagar Tsohon Gwamna Sun Fice daga Jam'iyyar
- Jam'iyyar APC a jihar Osun ta nuna cewa ko a jikinta ba ta damu da ficewar da ƙungiyar Omoluabi ta yi baya daga cikinta
- Ƙungiyar Omoluabi dai wacce ke ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, ta tattara ƴan komatsanta ta fice daga APC
- APC ta bayyana cewa ficewarsu ta buɗe hanyar kawo ƙarshen tarihinsu a siyasance kuma ko kaɗan ba ta damu da matakin da suka ɗauka ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Osun - Jam’iyyar APC reshen Osun ta mayar da martani ga ƙungiyar Omoluabi , wata ƙungiyar siyasa ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar, Rauf Aregbesola.
A ranar Lahadi, 26 ga watan Janairun 2025, ƙungiyar Omoluabi ta sanar da ficewa daga jam’iyyar APC.

Asali: Facebook
APC ta maidawa Omoluabi martani
Daraktan harkokin yaɗa labarai na APC a jihar Osun, Kola Olabisi, ya maida martani kan ficewar ƙungiyar Omoluabi cikin wata sanarwa a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daraktan yaɗa labaran na APC ya ce jam’iyyar ta ɗauki matakin Omoluabi na ficewa daga cikinta a matsayin rabuwa da ƙaya.
Kola Olabisi ya bayyana matakin ƙungiyar a matsayin buɗe hanyar kawo ƙarshen tarihinsu a siyasance, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Mai magana da yawun na APC ya tunatar da cewa yawancin mambobin ƙungiyar Omoluabi, sun riga sun fice ko an kore su daga jam’iyyar, inda ya bayyana su a matsayin wakilan jam’iyyar PDP.
“Muna cikin farin ciki a APC ta Osun da ganin bayan waɗannan ƴan barandan siyayar waɗanda tuni sun bar jam’iyyar a zuciya da jiki kafin zaɓen gwamna na 2022."
“Ba mu damu da matakin waɗannan ƴan siyasar da ta ƙare musu ba, waɗanda tun kusan shekaru uku da suka wuce suka fice daga jam’iyyar, bayan ƙoƙarinsu na ƙwace ikon shugabanci ya ci tura."
“Sanarwar baya-bayan nan ta cewa za ku kafa ko shiga wata jam’iyya daban, ita ce farkon ƙarshen siyasar ku, wacce za ta ƙare ta hanyar shafe tarihinku a zaɓen gwamna na 2026."
“Abin takaici, magoya bayan da ba su da hangen nesa a cikin ƙungiyar Omoluabi za su yi nadamar shiga wannan soki burutsun."
- Kola Olabisi
Aregbesola na rikici da jam'iyyar APC
Tun daga shekarar 2021, ɓangaren Rauf Aregbesola ya kasance yana rikici da reshen APC ta jihar kan tsarin shugabancin jam’iyyar.
Matsalar shugabanci a cikin APC ta Osun ta taimaka wajen jefa jam’iyyar cikin matsala, wanda hakan ya kai ga rashin nasararta a zaɓen gwamnan jihar na 2022.
APC ta dakatar da Aregbesola a Osun
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC a jihar Osun ta ɗauki matakin ladabtarwa kan tsohon gwamnan jihar, Rauf Aregbesola.
Jam'iyyar APC ta dakatar da tsohon gwamnan ne bisa zargin kawo rigima a cikinta da yi mata cin dunduniya a lokacin zaɓen gwamna na 2022.
APC ta zargi Aregbesola ta ƙoƙarin raba ta gida biyu bayan ya samar da ɓangarori biyu masu gaba da juna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng