'Ni Kadai Ke da Iko': Gwamnan APC Ya Rikita Zaman Makoki, Ya Gargadi Maciya Amana
- Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya gargadi masu neman kawo masa cikas a cikin mulkinsa inda ya ce su yi hakuri sai bayan shekaru takwas
- Gwamna Alia ya bayyana kansa a matsayin gwamnan jihar Benue kadai, yana mai gargadin masu ta da zaune tsaye da su nisanci jihar
- Alia ya jaddada shirinsa na tallafawa manoma tare da samar da kayan noma da irin shuka domin dawo da walwala ga al’ummar jihar Benue
- Gwamnan ya yi kira ga ’yan siyasa masu mummunar niyya su guji tada rikici, yana mai kira ga jama’a su zauna lafiya da juna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Makurdi, Benue - Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue ya bayyana kansa a matsayin gwamnan jihar Benue mai cikakken iko.
Gwamnan ya gargadi masu neman ta da rigima a jihar da su nisance ta har sai bayan ya kammala wa'adinsa na tsawon shekaru takwas.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

Asali: Facebook
Gwamna Alia ya jaddada karfin ikon mulkinsa
Gwamna Alia ya fadi haka ne yayin jawabinsa a jana'izar basaraken gargajiyar a Mbaede, karamar hukumar Vandeikya, cewar rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya tunatar da mutane cewa shi ne kaɗai gwamnan jihar ba tare da wani da ke da iko a jihar ba inda ya ce kowa ya yi zuwa nan da shekaru takwas.
Ya mayar da martani ga masu kokarin raina mulkinsa da cewa:
“Ni kadai ne gwamnan jihar Benue a yanzu."
“A nan Vandeikya, gaba daya kasar Tiv, ni ne Gwamna, idan ba ku so ba, ku bar jihar har bayan shekara takwas bayan wa’adina.”
“A nan Vandeikya, karamar hukumata, ku zo ku ayyana kanku a matsayin Gwamna sai idan ban ji ba."
- Hyacinth Alia
Gwamna Alia ya yi kira ga jama’a su rungumi zaman lafiya su kuma zauna lafiya da juna, yana mai gargadin ’yan siyasa masu mummunar niyya su guji tada fitina.
Gwamna ya sha alwashin tallafa wa manoma
Ya ce zai ci gaba da tallafawa manoma domin dawo da walwala, ta hanyar samar da kayan aikin noma da irin shuka domin bunkasa harkar noma.
Alia ya bayyana cewa mutanen Benue sun sha wahala a hannun ’yan siyasa marasa kishin kasa, yana mai cewa lokaci ya yi da za a jagoranci mutane cikin nagarta da shirye-shiryen da za su sa su dogara da kansu.
Ya yaba wa marigayin basaraken gargajiyar sa a matsayin mutum mai son zaman lafiya da kishin al’ummarsa, yana mai addu’a ga Allah ya ji kansa.
Gwamna Alia ya fatattaki ma'aikata a jihar
A baya, kun ji cewa Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia, ya kai ziyarar bazata sakatariyar jihar inda ya gano yadda ma'aikata ke wasa da aikinsu.
Mai girma Rabaren Hyacinth ya kulle daruruwan ma’aikata yayin ziyarar a sakatariyar, inda ya samu ma’aikata ‘yan kadan.
Ya nuna takaicinsa kan halin ma’aikata yayin da yake ziyartar ma’aikatu, yana mai bayyana damuwa kan rashin aiki da gaskiya.
Asali: Legit.ng