Jigon APC Ya Watsawa Gwamnan PDP a Arewa Kasa Ido, Ya Ki Amincewa da Tayin Muƙami
- Dan gwagwarmaya, Rikwense Muri a jihar Taraba, ya ki karbar muƙami da Gwamna Agbu Kefas ya yi masa a matsayin hadimi kan ayyuka
- Muri, wanda dan jam’iyyar APC ne, ya ce ya ki karbar nadin ne bayan tuntuba da shugabannin siyasa da jama’arsa saboda dalilai daban-daban
- Ya yaba da kokarin Gwamna Kefas na jawo kowa a mulki, amma ya ce yana da aminci ga manufofin jam’iyyar APC da shugaba Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jalingo, Taraba - Wani dan gwagwarmaya a Jihar Taraba, Rikwense Muri, ya ki karbar nadin mukami da Gwamna Agbu Kefas ya ba shi.
Rikwense Muri ya yi fatali da mukamin gwamnan a matsayin Mataimaki na Musamman (SSA) kan Bibiyar Ayyuka.

Asali: Twitter
Dan APC ya yi watsi da tayin mukami

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
Muri ya sanar da shawararsa ne a ranar Juma’a 24 ga watan Janairun 2025 a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata wasika da ya aika wa Gwamna Kefas ta hannun Sakataren Gwamnati na Jihar (SGS), Timothy Kataps, Muri ya yi godiya ga gwamnan kan damar da ya ba shi.
Matashin ya bayyana cewa ya ki karbar nadin ne bayan ya tattauna da jam’iyyarsa ta APC, shugabannin siyasa, da abokan huldarsa, tare da bayyana dalilai daban-daban.
Sai dai ya nuna godiyarsa ga nadin da gwamnan ya yi masa, tare da yaba wa kokarin Gwamna Kefas na jawo kowa da kowa a cikin mulkin jihar.
“Na rubuto domin bayyana godiya ta daga zuciya bisa wannan babbar dama da aka ba ni na zama Mataimaki na Musamman kan Bibiyar Ayyuka.
“A matsayi na na dan jam’iyyar APC tun 2015, na yi aiki tukuru wajen bunkasa jam’iyyar daga adawa zuwa jam’iyya mai mulki a mazabata.

Kara karanta wannan
'Babban abu na shirin faruwa': Martanin yan Najeriya da Peter Obi ya ziyarci jigon APC a Kano
“Wannan tsarin bai bi dokokin jam’iyyar ba, kuma ban shirya barin jam’iyyar APC ba a wannan lokaci."
- Rikwense Muri
Muri ya fadi dalilin kin karbar muƙami
Muri ya ce gwamna ya nuna karfin hali da adalci wajen nadin masu cancanta ba tare da la’akari da jam’iyyar su ba, amma ya ce ya gwammace ya ci gaba da biyayya ga APC.
Ya kara da cewa matsayinsa na jigo a APC, musamman Sakatare na Jama’a na Matasa na APC a jihar, yana da muhimmanci a gare shi.
Ya ce dalilan sun hada da gudummawar gwamnatin shugaba Bola Tinubu ga jihar Taraba, musamman ta fannin ayyukan gine-gine da sauran shirye-shirye na ci gaba.
Muri ya kuma ambata dokar da ke cikin kundin tsarin mulkin APC da ke hana karbar mukamai daga jam’iyyun adawa ba tare da izini daga babban ofishin jam’iyyar ba.
Gwamna Kefas ya samu goyon baya a 2027

Kara karanta wannan
'Neman gwamna ba zunubi ba ne': Kakakin Majalisa da aka tsige ya fadi dalilin taso shi a gaba
Kun ji cewa Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya fara samun goyon baya tun kafin ya ayyana takarar neman zango na biyu a zaɓen 2027.
Ƴan fansho na jihar Taraba sun bayyana gamsuwarsu da salon mulkin Kefas, sun ce ya cancanci ya samu wa'adi na biyu a zaɓe mai zuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng