Dele Momodu Ya Gaji da Hakuri, Ya Tona Abubuwa 2 da Suka Hargitsa PDP Tun Asali

Dele Momodu Ya Gaji da Hakuri, Ya Tona Abubuwa 2 da Suka Hargitsa PDP Tun Asali

  • Babban jigo a PDP, Dele Momodu ya bayyana tushen rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a babbar jam'iyyar adawa tun kakar zaɓen 2023
  • Momodu ya ce rikicin da ya hana PDP zaman lafiya ya samo asali ne daga zaben fidda gwani da kuma katsalandan da APC ke yi wa ƴan adawa
  • Ya ce tun da Wike ya sha kaye hannun Atiku kuma aka hana shi takarar mataimakin shugaban ƙasa, PDP ba ta sake zama lafiya ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wani jigon PDP, Dele Momodu, ya danganta tushen rikicin da jam’iyyar ke fama da shi zuwa abubuwa guda biyu.

Momodu ya ce rikicin PDP ya samo asali ne daga rashin warware sabani da aka samu a zaɓukan fidda gwani na 2022 da kuma zargin katsalandan daga APC mai mulki.

Kara karanta wannan

"Ba kamar Tinubu ba": Amaechi ya fadi yadda ya shirya samar da sauki ga talaka

Dele Momodu.
Dele Momodu ya ce zaben fidda ɗan takarar shugaban kasa da APC ne suka haddasa rigima a PDP Hoto: Dele Momodu
Asali: Facebook

Ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi shi a gidan talabijin na Arise tv ranar Alhamis, 23 ga watan Janairu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwan da suka hargitsa jam'iyyar PDP

Momodu, wanda ya nemi tikitin shugaban ƙasa na PDP gabanin zaɓen 2023, ya ce rikicin cikin gida ya fara ne bayan tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sha kaye a zaben fidda gwani.

A cewarsa, wannan kaye da Wike ya sha hannun Atiku kuma rashin zaɓensa a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban kasa ne tushen rigimar da ke faruwa a PDP.

“Rikicin ya fara ne tun lokacin da tsohon hwamna Wike ya sha kaye hannun Atiku Abubakar a zaben fidda gwani da kuma neman tikitin mataimaki."
"Yau ga shi ya koma jikin APC kuma ya kawo yanzu bai samu ya shiga cikinta ba ne saboda ya san ba zai samu ƙarfin ikon da yake da shi a PDP ba.

Kara karanta wannan

Bayan kiran El Rufa'i, Peter Obi ya ce ya yarda da hadakar 'yan adawa a 2027

"A halin yanzu, yana goyon bayan abokansa da suke da ƙarfi, yana karfafa musu gwiwa su ci gaba da riƙe PDP a ƙasa.”

- Dele Momodu.

APC na da hannu a rikicin PDP

Momodu ya ƙara da cewa akwai hannun wasu daga gefe musamman na APC wacce ke ƙulla rikici a jam’iyyun adawa don ci gaba da juya akalar ƙasar nan.

"A bayyane take Najeriya ta kama hanyar zama kasa mai jam'iyya ɗaya, APC ta tsorata adawa ta yi wa jam'iyyu lahani sosai domin har yanzu tana haɗa rigima a jam'iyyun adawa."
"Musamman manyan jam'iyyun adawa kamar PDP, LP da NNPP, a bayyane yake APC na da hannu a rigingimun cikin gida da ke faruwa a cikinsu," in ji shi.

Taya za a warware rikicin PDP?

Jigon siyasar ya musanta zargin cewa matsalolin PDP sun samo asali ne daga rashin cancanta, rashin manufa ko hadin kai.

Kara karanta wannan

Dogara ya tona asirin 2019: "Yadda Wike ya taimaki Bala ya zama gwamnan Bauchi a PDP"

A maimakon haka, ya yi ikirarin cewa tasirin jam’iyya mai mulki ya taka muhimmiyar rawa wajen jefa PDP cikin wannan hali.

Wani jigon PDP, Abdullahi Kabir ya shaidawa Legit Hausa cewa a yanzu babu abim da jam'iyyar take buƙata face haɗin kai da zaman lafiya.

Ya ce batun inda aka samu matsala tun farko ba shi ba ne mafita, hanyar da za a warware wannan rikici ya zama tarihi shi ne abin maida hankali.

"Gaskiya ya faɗi tun daga zaɓen fidda gwani aka fara samun matsala, amma ba shi ya kamata mu maida hankali ba, abin da ya wuce ya wuce, taya za mu kashe wutar rikicin nan?"
"Ni ina ganin mafita ita ce kowane ɗan PDP ya ajiye ra'ayinsa a gefe, mu kalli ƙasarmu, mu jingine duk wani banbanci mu haɗa kanmu, muna da dama a 2027," in ji shi.

Damagum ya ƙara samun goyon baya

A wani labarin, kun ji cewa mataimakan shugabannin PDP na kasa sun syyana goyon bayansu ga shugabancin muƙaddashin shugaban jam'iyya, Umar Damagum.

Ta bakin mataimakin shugaban matasa, jiga-jigan sun ce ba wanda ya iss ya tsige Damagum daga kujerar shugaban PDP sai wa'adinsa ya ƙare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262