Gwamnan Bauchi Ya Yi Wankin Babban Bargo ga Wike kan Tinubu
- Gwamna Bala Mohammed ya mayar da martani kan kalaman ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, da ya bayyana su a cikin wata hira da manema labarai
- Gwamnan ya yi kira ga Wike da ya rungumi gaskiya da da’a a siyasa maimakon ya rika nuna rashin kwarewa da rarraba kawuna
- Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Bauchi na ci gaba da samun nasarori a karkashin jagorancinsa, inda ya fifita shugabanci na gaskiya fiye da son zuciya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban gwamnonin PDP, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana damuwarsa kan wasu kalaman ministan birnin tarayya, Nyesom Wike.
A cewar gwamnan, kalaman Wike sun kasance cike da rarrabuwar kawuna, nuna son kai, da rashin martaba jam’iyyar PDP, wadda ta ba shi damar samun matsayinsa a siyasa.

Kara karanta wannan
Dogara ya tona asirin 2019: "Yadda Wike ya taimaki Bala ya zama gwamnan Bauchi a PDP"

Source: Twitter
Hadimin gwamna Bala Mohammed ya wallafa a Facebook cewa gwamnatin Bauchi ta yi martani ne bayan kalaman da Nyesom Wike ya yi a wata hira da manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bala Mohammed ya ce bai kamata a bar irin wannan dabi’a ta ci gaba da wanzuwa ba, domin hakan na barazana ga hadin kan jam’iyya da kuma ci gaban dimokradiyya a kasar nan.
Magana kan alakar Wike da PDP
Sanata Bala Mohammed ya bayyana Wike a matsayin dan siyasa mai nuna son kai, wanda ya manta da irin goyon bayan da jam’iyyar PDP ta ba shi a lokacin da yake fama a siyasarsa.
Punch ta ruwaito gwamnan na cewa;
“Ba abu mai kyau ba ne a ga mutum yana cin moriyar wata jam’iyya amma kuma ya yi kokarin rusa ginshikinta. Wannan dabi’a ce da ba za ta haifar da alheri ba.”

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
Bala Mohammed ya kara da cewa siyasarsa ta ginu ne kan gaskiya da kishin jama’a, ba kan nuna kwarewa a rarraba kawuna da yin amfani da mutane domin cimma muradin kansa ba.
Abota tsakanin Bala Mohammed da Wike
Gwamnan Bauchi ya yi watsi da zargin da Wike ya yi na cewa ba su da alaka ta abota, yana mai cewa abota ba ita ce ginshikin nasara a shugabanci ba.
“Shugabanci yana buƙatar kwarewa, hangen nesa, da iya aiwatar da ayyukan al’umma.
Kalaman Wike game da abota basu da wani tasiri a ayyukan ci gaban da nake yi a jihar Bauchi,”
- Bala Mohammed
Gwamnan ya bayyana nasarorin da gwamnatin Bauchi ta samu a fannonin tattalin arziki, ilimi, da lafiya, wanda ya ce suna nuni da irin himma da jajircewar gwamnatinsa.
Magana kan kudirin harajin Tinubu
Bala Mohammed ya kuma maida martani kan zargin da Wike ya yi na cewa ya yi adawa da kudirin harajin gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cewar gwamnan, wannan adawar ba ta da alaka da son zuciya, sai domin tabbatar da cewa dokokin sun yi daidai da bukatun jama’a.
“Wike yana magana ne ba tare da yin la’akari da gaskiya ba.
Amma mu a PDP muna da alhakin kare muradun talakawa kuma muna yin hakan ta hanyar tattaunawa da gwamnati kan dokokin da za su kawo cigaba mai dorewa,”
- Bala Mohammed
Zargin rashin kwarewa a matsayin minista
Sanata Bala ya bayyana damuwarsa kan yadda Wike ya mayar da aikin minista tamkar wata fage ta yin hayaniya da zubar da kimar gwamnati.
Gwamnan ya ce;
“Maimakon amfani da ofishinsa wajen haɗa kan al’umma, Wike yana amfani da shi wajen yin hayaniya mara ma’ana da wuce gona da iri.”
Bala Mohammed ya yi kira ga Wike da ya rungumi shugabanci mai kima, ya kuma kauce wa nuna rashin da’a da ake gani a wasu daga cikin ayyukansa.
Sauyin da aka yi wa kudirin haraji
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin Najeriya sun yi kwaskwarima ga kudirin harajin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnonin sun sauya yadda za a rika raba harajin VAT ga jihohi duk wata sabanin yadda shugaba Tinubu ya bukata a karon farko.
Asali: Legit.ng
