An Shiga Fargaba da 'Yan Sanda Suka Mamaye Sakatariyar PDP, Sun Rufe Hanyar Shiga

An Shiga Fargaba da 'Yan Sanda Suka Mamaye Sakatariyar PDP, Sun Rufe Hanyar Shiga

  • Rikici ya barke a PDP jihar Rivers yayin da ‘yan sanda suka toshe hanyar zuwa sakatariyar jam’iyyar da ke kan titin Aba
  • Rahoto ya nuna cewa 'yan sanda sun je dakile tarzoma ne bayan da aka ji cewa wani tsagi na jam'iyyar zai kwace ikon sakatariyar
  • Rikicin jam'iyyar dai ya kara tsananta ne yayin da bangarorin biyu ke nuna iko da shugabanci bayan hukuncin kotu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rivers - Rikici ya barke a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers, a ranar Alhamis yayin da ‘yan sanda suka toshe hanyar zuwa sakatariyar PDP.

An rahoto cewa 'yan sanda sun mamaye sakatariyar ne da ke kan titin Aba biyo bayan rahotannin da ke cewa rigima ta barke kan shugabancin jam'iyyar.

'Yan sanda sun toshe hanyar shiga sakatariyar PDP yayin da rikici ya barke a Ribas
Rikicin cikin gida ya barke a jam'iyyar PDP a Ribas, 'yan sanda sun hana shiga sakatariya. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Rivers: Rikici ya barke a jam'iyyar PDP

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da 'yan ta'addar Lakurawa suka kashe sojojin Najeriya 5

Jaridar Punch ta rahoto cewa kwamitin rikon kwarya, wanda aka kafa bayan kotu ta rushe shugabancin zabe, yana shirin kwace sakatariyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Litinin, babbar kotun jihar Rivers da ke Fatakwal ta rushe zaben PDP na matakan gunduma, kananan hukumomi, da na jiha na 2024.

Duk da cewa an dakatar da shirin kwace sakatariyar, bangarorin biyu sun gudanar da tarukan manema labarai daban-daban don nuna ikonsu, lamarin da ya kara rikicin.

Tsagin Chukwuemeka za su daukaka kara

Magoya bayan jam’iyyar sun taru a ciki da wajen sakatariyar, lamarin da ya nuna irin yadda yanayin ya yi zafi, inji rahoton Channels TV.

Aaron Chukwuemeka, shugaban kwamitin da aka dakatar, ya soki yawaitar shari’o’in da suka shafi jam’iyyar, yana rokon Gwamna Siminalayi Fubara ya dawo da zaman lafiya.

Lauyan PDP na jihar, Kingsley Chuku (SAN), ya bayyana cewa jam’iyyar tana shirin daukaka kara bayan samun cikakken bayanin hukuncin kotu.

Kara karanta wannan

'Sun nemi N25m': Ƴan sanda sun kama mutanen da suka kashe yaro a Katsina

Chukwuemeka da Chuku sun zargi wasu mambobin kwamitin rikon kwarya da kasancewa ‘yan jam’iyyar APP, suna ikirarin cewa ba su da hurumin jagorantar PDP.

Tsagin Robinson su fasa kwace sakatariya

A wani taro daban, Robinson Nname-Ewor, shugaban rikon kwarya na PDP, ya bayyana cewa sun dakatar da shirin kwace sakatariyar don kauce wa rikici.

Sai dai ya gabatar da bukatu don magance rikicin jam’iyyar, ciki har da dawo da shugabanci karkashin Fubara da amincewa da kwamitin rikon kwarya na jihar.

Nname-Ewor ya kuma bayyana shirin kafa kwamitin ladabtarwa don binciken zarge-zargen cin amanar jam’iyya, musamman wadanda suka shafi zaben 2023.

PDP ta sake samun wani shugaban riko

Duk da dakatar da shirin kwace sakatariyar, har ana samun rashin jituwa da tashin hankali wanda ke kara nuna cewa rikicin Rivers PDP bai kare ba.

Rikicin PDP a jihar Rivers ya tsananta a ranar Laraba yayin da shugabannin bangarorin biyu suka fito, lamarin da ya tilasta 'yan sanda daukar mataki.

Kara karanta wannan

Shugabannin PDP da APC sun harbi juna da maganganu bayan hari a kotun Edo

Shugaban PDP na mazabar Yammacin Rivers, Robinson Ewor, ya ayyana kansa a matsayin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar reshen jihar.

Rivers: 'Yan majalisar PDP sun rasa kujerunsu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Tsagin majalisar dokokin jihar Ribas da ke tare da Nyesom Wike sun bayyana kujerun ƴan majalisa huɗu a matsayin babu kowa.

Kakakin majalisar, Martin Amaewhule, ya ce an ɗauki matakin ne saboda rashin halartar zaman majalisa na kwanaki 152 da rikicin siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.