2027: Rikici Ya Barke tsakanin Gwamnan Bauchi da Ministan Tinubu

2027: Rikici Ya Barke tsakanin Gwamnan Bauchi da Ministan Tinubu

  • Gwamnatin Bala Mohammed ta musanta zarge-zargen Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, tana mai cewa zance aka kirkira domin bata suna
  • Jami'an gwamnatin sun fadi ci gaban da aka samu a fannoni kamar ilimi, kiwon lafiya, da ababen more rayuwa a lokacin mulkin Sanata Bala Mohammed
  • Gwamnatin Bauchi ta zargi gwamnatin tarayya da amfani da zarge-zarge domin kawo cikas ga gwamnan saboda tsare-tsaren siyasar shekarar 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Gwamnatin Bauchi karkashin jagorancin Sanata Bala Mohammed ta mayar da martani kan zarge-zargen da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya mata.

Hadimin gwamna Bala Mohammed, Lawal Muazu Bauchi, ya bayyana cewa zarge-zargen ba su da tushe, kuma an kirkire su ne domin bata sunan gwamnan.

Kara karanta wannan

Abba ya kwato motocin da jami'an gwamnatin Ganduje suka tsere da su a Kano

Gwamnatin Bauchi
Gwamnan Bauchi ya yi raddi ga ministan Tinubu. Hoto: Lawal Mu'azu Bauchi|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A cikin sakon da ya wallafa a Facebook, hadimin gwamnan ya ce kalaman Tuggar na da nasaba da tsare-tsaren siyasa da aka kawo domin rage darajar gwamna Bala Mohammed a idon jama’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bauchi: Martani ga Tuggar kan ilimi

Bayan kalaman Tuggar, gwamnatin Bauchi ta ce an samu ci gaba mai girma wajen rage yawan yaran da ke zama a gida ba tare da zuwa makaranta ba a karkashin gwamnatin Bala Mohammed.

Gwamnatin ta ce ta samar da shirin mayar da yara makaranta wanda ya sa yara sama da 500,000 suka koma makaranta cikin shekaru biyu.

Mai ba gwamnan shawara ya ce shirin ya samu goyon bayan sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi, wanda hakan ya tabbatar da aniyar gwamnan wajen bunkasa ilimi.

Cigaban da aka samu a wasu sassa

Gwamnatin ta bayyana cewa an samu cigaba a fannoni kamar kiwon lafiya, ababen more rayuwa, da kuma aikin gona.

Kara karanta wannan

Tinubu ya jaddada shirin ragargazar 'yan ta'adda a fadin Najeriya

Sabanin zargin Tuggar, gwamnatin ta ce ta gina dubban ajujuwa, gyaran makarantu, da kuma shirin saukaka wa al’ummar jihar samun ingantaccen kiwon lafiya.

A cewar mai taimakawa gwamnan a sha'anin sadarwan zamani, shirin ya kara inganta rayuwar jama’a da kuma tabbatar da kyakkyawar makoma ga jihar.

Tuggar ya jefo zargin cin hanci a jihar Bauchi

Gwamnatin Bauchi ta musanta zarge-zargen da ake yi wa Bala Mohammed na cin hanci da karbar filaye ba bisa ka’ida ba.

An bayyana cewa gwamnatin jihar na gudanar da ayyuka ne cikin gaskiya da rikon amana, inda kudi suke tafiya kai-tsaye wajen amfanar al’umma.

A cewar Lawal Muazu, zarge-zargen Tuggar wani yunkuri ne na karkatar da hankalin jama’a daga nasarorin da aka samu a gwamnatin Bauchi.

Tuggar
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar. Hoto: Federal Ministry of Foreign Affairs, Nigeria
Asali: Facebook

Zargin gwamnatin Bauchi kan siyasar 2027

Gwamnatin Bauchi ta bayyana cewa zarge-zargen Yusuf Tuggar na dauke da alamar siyasa, inda ake ganin akwai matsin lamba daga gwamnatin tarayya domin rage tasirin Bala Mohammed.

Kara karanta wannan

"Ku maida Hausa yaren koyarwa a makarantu," Gwamna ya ba gwamnonin Arewa shawara

An yi zargin cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya umurci Tuggar ya saka Gwamna Bala Mohammed a gaba domin raunata adawarsa ga siyasar 2027.

Kudirorin gwamna Bala Mohammed

Duk da wadannan kalubale, Gwamna Bala Mohammed ya jaddada kudirinsa na ci gaba da yi wa mutanen Bauchi aiki tukuru.

Gwamnan ya yi alkawarin cewa ba zai bari wani abu ya karkatar da shi daga aniyarsa ta tabbatar da ci gaba mai dorewa a jihar.

Gwamnatin ta yi kira ga shugaba Tinubu da ya dakatar da amfani da ministansa wajen kawo cikas ga gwamnonin da ke aiki tukuru, kamar Gwamna Bala Mohammed.

Bola Tinubu ya yi martani ga Sarki Sanusi II

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi martani ga mai martaba Muhammadu Sanusi II kan maganar da ya yi game da tsare tsaren Bola Tinubu.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya yi Allah wadai da kalaman Sanusi II, ya ce bai kamata sarkin ya rika sukar tsare tsaren da ya amince da su ba a baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng