Rikici Ya Sake Kacamewa a PDP, Sabon Shugaban Jam'iyya Ya Bayyana
- Rikicin PDP reshen jihar Ribas ya ɗauki sabon salo bayan babbar kotu ta tsige shugabannin jam'iyyar na tsagin ministan Abuja, Nyesom Wike
- Robinson Ewor ya bayyana kansa a matsayin muƙaddashin shugaban PDP na Ribas tare da sanar da sabon kwamitin shugabanci na rikon ƙwarya
- Ewor ya zargi Nyesom Wike da magoya bayansa da yin katsalandan a umarnin PDP ta ƙasa, wanda ya ce ya haifar da rikicin shugabanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Rigingimun cikin gida da suka dabaibaye jam'iyyar PDP a jihar Ribas ya ƙara tsanani yayin da aka ƙara samun sabon shugaban jam'iyya
Hakan ya biyo bayan hukuncin kotu da ya rusa zabukan da suka samar da shugabannin PDP masu biyayya ga ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike.
Kotu ta tsige shugabannin PDP a Ribas
The Nation ta rahoto cewa a ranar 13 ga watan Janairu, 2025, babbar kotun jihar Ribas da ke zama a Fatakwal ta tsige shugabannin PDP da aka zaɓa a tarukan da suka gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ƙarƙashin Mai Shari’a Stephen Jumbo, ta bayar da umarnin soke zaɓen shugabannin PDP a matakan gunduma, ƙananan hukumomi da jiha.
Alkalin ya ba da umarnin hana dukkan shugabannin PDP na jihar Ribas ƙarƙashin Aaron Chukwuemeka, ci gaba da aiki a matsayin jagororin jam'iyya
Wannan umarni ya biyo bayan karar da Edwin Woko, Love Otuonye da wasu mutum biyu suka shigar gaban kotun.
Sabon shugaban PDP na riƙo ya bayyana
Bayan hukuncin kotun, shugaban PDP na Ribas ta yamma, Robinson Ewor, ya bayyana kansa a matsayin muƙaddashin shugaban jam’iyyar.
A wani taron manema labarai da ya yi a Fatakwal, Ewor ya sanar da Dr. Feild Nkor a matsayin sakataren riƙo tare da bayyana sauran shugabannin kwamitin riƙon kwarya
Waɗanda ya kira a matsayin yan kwamitin rikon ƙwarya na PDP a jihar Ribas sun haɗa da Uranta Humphrey, Sydney Gbara, Victor Pepple, da Emile Solomon.
Zargin canja umarnin PDP ta ƙasa
A jawabinsa, Ewor ya zargi Wike da magoya bayansa da yin katsalandan a umarnin da ya fito daga hedkwatar PDP ta kasa wanda ya tsawaita wa’adin tsoffin shugabanni.
Ya kuma bayyana cewa hukuncin kotu ya maido da shugabancin jam’iyyar ga waɗanda ya kira “masu gaskiya” ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar, Siminalayi Fubara.
Kalubale ga shugabancin Aaron Chukwuemeka
Bugu da ƙari, Ewor ya ƙalubalanci tsagin Aaron Chukwuemeka da Martin Amaewhule, inda ya kira su haramtattun shugabanni.
"Hukuncin kotu ya hana Aaron Chukwuemeka da magoya bayansa gabatar da kansu a matsayin shugabannin PDP a matakai daban-daban a jihar Ribas," in ji shi.
Bayyana sabon mukaddashin shugaban PDP ya kara jefa jam'iyyar cikin ruɗani da rikici mai tsanani bayan hukuncun da kotu ta yanke.
Rikicin PDP: Wike ya maida martani ga Odili
Kuna da labarin cewa ministan Abuja, Wike ya caccaki tsohon gwamnan jihar Ribas, Peter Odili, ya ce shi ke zuga Simi Fibara ya take umarnin Bola Tinubu.
Wike ya kuma bugi ƙirji da cewa tun da aka kafa jihar Ribas, ba a taba gwamnan ya kawo ci gaba kamarsa ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng