Gwamna Ya Kori Kwamishinoni da Dukkan 'Yan Majalisar Zartarwa
- Rahotanni na nuni da cewa gwamnan Ondo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya amince da rusa majalisar zartarwar jihar da yake mulki
- An bar kwamishinan shari’a, Kayode Ajulo da kwamishinar kudi, Omowunmi Isaac, saboda mahimmancin ayyukansu a gwamnati
- Matakin na zuwa ne bayan gwamnan ya samu nasarar lashe zabe karo na biyu, wanda ake gani a matsayin shiri na kafa sabuwar tafiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo - Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa, ya sanar da rusa majalisar zartarwar jihar a yau Laraba.
Gwamnan ya bayar umarni ga dukkan mambobin majalisar da lamarin shafa su mika dukkan abubuwan gwamnati da ke hannunsu.
Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da mai magana da yawun gwamnan, Ebenezer Adeniyan ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Ondo ya rusa majalisar zartarwa
A yau Laraba, 15 ga watan Janairu gwamna Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya rusa majalisar zartarwar jihar Ondo.
Kakakin gwamnan, Prince Ebenezer Adeniyan ne ya fitar da sanarwar yayin da ake tsaka da bikin tunawa da 'yan mazan jiya a fadin Najeriya.
Wannan mataki ya shafi dukkan mambobin majalisar ban da mutum biyu da suka hada da kwamishinan shari’a, Dr Kayode Ajulo, da kwamishinar kudi, Omowunmi Isaac.
Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamnan zai cigaba da tafiya da kwamishinonin kudi da shari'a saboda mahimmancin ayyukansu a harkokin gwamnati.
Umarnin mika kayan gwamnati
An umarci dukkan mambobin majalisar da lamarin shafa su mika kayan gwamnati da ke hannunsu ga jami’an kula da kudi na ma’aikatunsu cikin gaggawa.
Wannan mataki ya kasance ne domin tabbatar da tsafta da bin doka a lokacin da ake aiwatar da sabbin tsare-tsaren gwamnatin jihar.
Haka zalika, gwamnan ya gode wa mambobin majalisar bisa gudunmawarsu ga ci gaban Jihar Ondo tare da yi musu fatan alheri a ayyukansu na gaba.
Ra’ayoyin jama’a kan matakin gwamnan
A cikin martanin da jama’a suka fara bayarwa kan matakin, ana ganin rusa majalisar zartarwar a matsayin wani yunkuri na kawo sababbin mutane cikin gwamnatin nasu a wa’adinsa na biyu.
Wasu daga cikin masu lura da al’amuran siyasa sun yaba wa gwamnan bisa irin wannan tunani, suna mai cewa hakan zai kawo karin himma a fannin gudanar da gwamnati.
Har ila yau, wasu matasan jihar Ondo sun bukaci gwamnan ya yi amfani da matasa domin a cewarsu za su tabukka abin kirki wajen gina sabuwar Ondo.
A wata mai kamawa ne za a rantsar da gwamna Lucky Aiyedatiwa domin fara wa'adi na biyu kamar yadda hadiminsa ya wallafa a Facebook.
Gwamna Aiyedatiwa ya yi godiya
Gwamna Aiyedatiwa ya yabawa mambobin majalisar bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen bunkasa Jihar Ondo a wa’adinsa na farko.
“Na gode wa dukkan mambobin majalisar bisa hidimar da suka yi wa jiharmu. Ina fatan za su ci gaba da yin aiki tukuru a duk inda suka tsinci kansu.”
- Gwamna Lucky Aiyedatiwa
An saka dokar hana fita a Ondo
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya sanya dokar hana fita a yankin Owo na jihar.
An ruwaito cewa lamarin ya faru ne sakamakon wani rikici da aka samu tsakanin kungiyoyin asiri da kuma kashe wani jigo a APC da aka yi a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng