Yadda aka gudanar da bikin tunawa da ýan mazan jiya a jihar Kaduna (Hotuna)
A ranar 15 ga watan Janairu ma kowane shekara ne ake gudanar da bikin tunawa tare da karrama mazan jiya, Sojojin da suka sha artabu a yakunan dasuka gabata, kamar yadda Legit.ng ta gano.
Wannan biki ana gudanar da shi a dukkanin kasashen Duniya, sai dai kowada ranakun da suke yin nasu bikin,a baya ana yin wannan biki ne a ranar 11 ga watan Nuwambar kowace shekara, don tunawa da Sojojin da suka fafata a yakin Duniya na biyu.
KU KARANTA: Sai na mulki Najeriya ko ta wani hali – Inji wani babban Fasto
Sai dai daga bisani ne aka sauya ranar zuwa 15 ga watan Nuwamba don tunawa da Sojojin da suka fafata a yakin basasan Najeriya, wato yakin Biyafara, wanda Sojoji suka kare mutuncin Najeriya na tabbatar da ta zauna kasa daya dunkulalliya.
Baya ga jihar Kaduna, ana gudanar da wannan biki a dukkanin jihohin Najeriya 36, har da babban birnin tarayya Abuja, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu halarta a yau.
A jawabinsa, gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ya jinjina ma Sojojin Najeriya bisa sadaukar da rayukansu don tabbatar da ganin jama'a sun zanuna lafiya cikin kwanciyar hankali.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng