Baraka a PDP Ta na Kara Ƙamari, Jigo Ya Haramta Shugabancin Damagun

Baraka a PDP Ta na Kara Ƙamari, Jigo Ya Haramta Shugabancin Damagun

  • Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa Umar Damagum yana rike da kujerar Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa ba bisa ka’ida ba
  • Ologbondiyan wanda jigo ne a babbar jam'iyyar adawar ya kara da cewa wannan daya ne daga tarin matsalolin da su ka sanya PDP a gaba a yanzu
  • Kusa a jam'iyyar ya yi zargin cewa wasu ƙungiyoyi daga waje suna ƙoƙarin tarwatsa PDP tare da mayar da ita reshe na jam’iyyar APC mai mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT Abuja - Jigo a jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya bayyana cewa Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Umar Damagum, yana kan wannan kujera ba bisa ka’ida ba.

Kola Ologbondiyan ya bayyana wannan ne a yayin da yake mayar da martani kan yadda wasu ƙungiyoyi daga waje ke ƙoƙarin lalata PDP.

PDP Official
Rikicin PDP ya na kara kamari Hoto: PDP Official
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa tsohon Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na PDP ya bayyana cewa ana ƙoƙarin mayar da PDP reshe na jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Bafarawa: Tsohon gwamnan jihar Sokoto ya fice daga jam'iyyar PDP, ya fadi dalili

Jam'iyyar PDP ta na cikin tsaka mai wuya, yayin da rigingimun shugabanci ya dabaibaye ta, a lokacin da ta ke neman hadaka da wasu manyan 'yan siyasar kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin PDP: Dalilin haramta shugabancin Damagun

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Ologbondiyan ya ce Damagum ya fito daga yankin Arewa maso Gabas, wanda yanzu haka kujerar a yankin ya dace ta zauna ba.

Mista Ologbondiyan ya tabbatar da cewa yankin Arewa ta Tsakiya ta na buƙatar a dawo da kujerar Shugaban Jam’iyyar gare su, kamar yadda ya ke a tsari.

A cewarsa:

“Wani karin magana ya ce, sai bango ya tsake kadangare ya ke samun wurin shiga.
"Akwai matsaloli a cikin jam’iyya, amma yadda ake sarrafa waɗannan matsaloli abu ne mai zaman kansa, sannan yadda tasirin wasu daga waje ke shiga cikin PDP don tarwatsa jam’iyyar shi ne wani al’amari ne daban."

"Akwai matsaloli a jam'iyyar PDP,” Ologbondiyan

Kara karanta wannan

Bayan korar mataimakin shugaban PDP na kasa, an naɗa wanda zai maye gurbinsa

Babban kusa a jam’iyyar adawa ta PDP, Kola Ologbondiyan ya tabbatar da cewa akwai manya-manyan matsaloli da jam’iyyar ke fuskanta ta bangarori da dama.

Ologbondiyan ya ƙara da cewa:

“Akwai matsaloli a PDP. Dangane da batun Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar, Arewa ta Tsakiya tana ganin ya dace a dawo musu da wannan kujera. Damagum daga Arewa maso Gabas yake, kuma yana rike da wannan matsayi ba bisa ka’ida ba.
“Ko da kuwa ya jima a kan wannan kujera, har yanzu shugabancinsa ba bisa ka’ida ba ne. Wannan babban matsala ce a jam’iyyar.”

PDP ta gano dalilin faduwarta zabe

A wani labarin, kun ji cewa PDP ta reshen jihar Abia ta bayyana cewa ta gano kurakuranta da suka jawo mata faduwa a zaben 2023, tare da daukar alwashin dawo da karfinta a kakar zaben 2027.

Shugaban PDP na jihar Abia, Elder Abraham Amah, ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a garin Abam, karamar hukumar Arochukwu, inda ya ce sun shirya tsaf.

Kara karanta wannan

PDP ta kama hanyar zama tarihi a Najeriya, an tono masu koƙarin kashe jam'iyyar

Elder Amah ya yi kira ga dukkan ‘ya’yan jam’iyyar da su yafewa juna tare da hada kai domin ceto PDP daga durkushewa yayin da ake ci gaba da nazarin matsalolin jam’iyyar don magance su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.