PDP Ta Gano Dalilin Faduwarta Zaben 2023, Ta Fadi Jihar da Take Son Kwacewa a 2027
- Jam’iyyar PDP ta gano dalilan da suka sa ta fadi zaben 2023 a jihar Abia, ciki har da tsayar da ‘yan takarar da basu cancanta ba
- Shugaban PDP na jihar Abia, Elder Abraham Amah, ya ce darasin faduwar zaben zai taimaka wajen dawo da martabar jam’iyyar
- Amah ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su yafewa juna tare da tabbatar da cewa PDP za ta kwace jihar daga APC a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abia - Jam’iyyar PDP reshen Abia ta bayyana cewa ta gano dalilan da suka sa ta sha kasa a zaben 2023 a jihar.
Jam’iyyar ta ce tana kan daukar matakan dawo da karfinta a jihar, musamman a mazabar sanatan Abia ta Arewa.
Shugaban PDP na Abia, Elder Abraham Amah, ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki na Abia ta Arewa da aka gudanar a garin Abam, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abia: PDP ta gano dalilin faduwarta zabe
Abam na cikin karamar hukumar Arochukwu, kuma shi ne garin Hon. Uko Nkole, tsohon dan majalisar wakilai na mazabar Arochukwu/Ohafia.
Abraham Amah ya bayyana cewa daya daga cikin dalilan da suka sa jam'iyyar PDP ta fadi zaben ya hada da almubazzaranci da sauran matsaloli.
Shugaban jam'iyyar ya ce:
“Mun san dalilan da suka sa muka fadi zaben. Ba saboda dalili daya muka fadi ba, akwai matsaloli da dama.
"Sabani tsakanin jam’iyya, tasirin Peter Obi, zaben ‘yan takarar da ba su dace ba, cin kudin jam’iyya - duka sun taimaka wajen faduwar mu."
"Za mu dawo da martabarmu" - Shugaban PDP
Abraham Amah ya bayyana cewa kwamitin ayyukan jam'iyyar na jihar ya yi nazari kan lamarin a kananan hukumomi biyar na Abia ta Arewa.
"A wasu yankunan, jam’iyyun APC, PDP da LP sun kwace tasirin siyasarmu sosai," inji Amah.
Sai dai ya tabbatar da cewa PDP ba za ta rasa kwarjininta gaba daya ba, yana mai cewa:
"Zamu dawo da martabar jam’iyyarmu, kuma mu sake cin zabe."
Shugaban PDP ya ce ya san jam’iyyar ta bata ran wasu mutane, amma akwai wadanda ke ci gaba da cin dunduniyarta duk da ba ayi masu laifin komai ba.
PDP ta koyi darasi bayan faduwa zaben 2023
Shugaban jam'iyyar ya fayyace gaskiya da cewa:
"Yan siyasa kan ji dadin abubuwa idan suna amfanarsu, amma idan abubuwa suka juya masu baya, sai kuma su dawo suna tada jijiyoyin wuya."
Ya gode wa Ubangiji da ya zaben 2023 ya zama wani babban darasi ga jam’iyyar PDP a jihar Abia.
"Idan ba mu fadi zaben ba, da ba za mu samu damar yin magana ko cin gajiyar wasu abubuwa ba," inji shugaban jam'iyyar.
Abraham Amah ya yi kira ga dukkanin 'yan jam'iyyar da su yafewa juna, yana mai tabbatar da cewa za su dawo mulki da ikon Allah a 2027.
Babban jigon PDP ya sauya sheka zuwa APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa PDP a jihar Abia ta sake fuskantar babbar matsaya yayin da wani kusanta da magoya bayansa 6,000 suka koma APC.
Fitaccen ɗan kasuwa a Abia, Cif Kelvin Jumbo Onumah ya tattara komatsansa tare da dubunnan magoya bayansa ya fice daga PDP zuwa APC.
Asali: Legit.ng