PDP Ta Kama Hanyar Zama Tarihi a Najeriya, An Tono Masu Kokarin Kashe Jam'iyyar

PDP Ta Kama Hanyar Zama Tarihi a Najeriya, An Tono Masu Kokarin Kashe Jam'iyyar

  • Mista Kola Ologbodiyan ya zargi APC mai mulkim Najeriya da yunƙurin mayar da jam'iyyar PDP tamkar wani rsehenta
  • Tsohon mai magana da yawun PDP na ƙasa ya ce naɗa Wike a matsayin minista a gwamnatin Tinubu barazana ce ga babbar jam'iyyar adawa
  • Ya buƙaci ƴaƴan PDP a dukkan matakai su maida wuƙarsu kube kuma su fahimci makircin da ake shirya masu da nufin ruguza jam'iyyarsu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon kakakin PDP na ƙasa, Kola Ologbodiyan ya zargi APC da kitsa duk wani rikicin cikin gida da ya hana babbar jam'iyyar adawa zaman lafiya.

Ologbodiyan ya goyi bayan ikirarin Debo Ologunagba, sakataren yada labarai na PDP ta ƙasa, wanda ya ce akwai wasu da ba ƴan PDP ba da suke rura wutar rikicin.

Kola Ologbodiyan.
Tsohon kakakin PDP ya zargi APC da hannu a duka rikicin da ke faruwa a babbar jam'iyyar adawa Hoto: Kola Ologbodiyan, APC Nigeria
Asali: Facebook

Ya yi wannan furucin ne a cikin shirin Arise TV mai taken, "The Morning Show" ranar Talata, 14 ga Janairu, 2025.

Kara karanta wannan

Bayan korar mataimakin shugaban PDP na kasa, an naɗa wanda zai maye gurbinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano yadda APC ke rura rikicin PDP

Ologbodiyan ya ce ya fahimci APC na da hannu kuma tana yunkurin gurgunta PDP ne domin ta ci gaba da jan ragamar ƙasar nan, rahoton Vanguard.

A cewarsa, nadin tsohon gwamnan Ribas Nyesom Wike, wanda shi ma ɗan PDP ne a matsayin ministan Abuja wani salo ne na gurgunta PDP daga cikin gida.

Ya ce wannan mataki na jawo Wike cikin gwamnafin APC yana iya zama babban barazana ga ci gaban jam’iyyar PDP.

Naɗin Wike barazana ce ga ci gaban PDP

Ologbodiyan ya ce:

“A kan batun tasirin waje daga APC ko shugabanninta, na dade ina bayyana ra’ayina cewa akwai yunƙuri daga APC na mayar da PDP tamkar reshe ko ɓangare na jam’iyyar.
“Haka zalika, shigar Nyesom Wike, wanda ya taba neman takarar shugaban kasa a inuwar PDP cikin gwamnatin APC wata matsala ce da ka iya yin tasiri sosai wajen gurgunta PDP, babu mai iya ƙaryata wannan.”

Kara karanta wannan

"Ku yi fatali da APC," CUPP ta ba ƴan Najeriya shawara da mafita a zaben 2027

Ologbodiyan ya ja hankalin ƴaƴan PDP kan muhimmancin tashi tsaye don kare martabar jam’iyyar daga makircin da ke ƙoƙarin rusa ta.

Ya kamata PDP ta haɗa kai wuri guda

Ya ce lokaci ya yi da kowa zai ba da gudummuwa wajen ƙarfafa haɗin kai da dagewa wajen ceto jam’iyyar daga duk wani haro da ake kawo mata daga waje.

Da yake tsokaci kan rikicin shugabanci musamman batun kujerar sakataren PDP na ƙasa, Ologbodiyan ya amince jam'iyyar na fama da wasu matsalolin cikin gida da ya kamata a magance.

Sai dai ya zargi wasu daga waje da ke amfani da wannan damar wajen kutsawa cikin jam'iyyar, tare da lalata tsarin PDP.

Ya kuma yi mamakin yadda rikicin ke daɗa ruruwa, yana mai cewa idan ba don wasu daga waje na zubawa wutar fetur ba, da tuni kwamitin gudanarwa na kasa ya warware matsalolin cikin sauƙi.

Kara karanta wannan

Shugaba a APC ya yi zazzafan martani ga El Rufa'i kan hadaka da 'yan adawa

PDP ta karyata rahoton sauya sheƙar ƴan Majalisa

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta musanta rahoton da ke yawo cewa waus ƴan majalisarta 12 na shirin sauya sheƙa a jihar Abia.

Shugaban PDP reshen Abia ya ce labarin karya ne, ƴan Majalisar ba su da shirin barin babbar jam'iyyar adawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262