"Ku Yi Fatali da APC," CUPP Ta ba Ƴan Najeriya Shawara da Mafita a Zaben 2027
- Gamayyar jam'iyyun siyasa a Najeriya watau CUPP ta yi tir da kisan gillar da ƴan Boko Haram suka yi wa manoma 40 a jihar Borno
- Ƙungiyar ta ce lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su yi fatali da APC a zaben 2027 domin idan ta ci gaba da mulki ba a san halin da za a shiga ba
- Sai dai duk da haka CUPP ta buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin ƴan Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gamayyar jam’iyyun siyasa ta ƙasa (CUPP), babbar ƙungiyar adawa a Najeriya, ta bayyana damuwarta kan ƙaruwar rashin tsaro da ke addabar ƙasar nan.
CUPP ta caccaki Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu bisa gazawa wajen kare rayukan al’umma.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar, Kwamared Mark Adebayo ya sanyawa hannu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CUPP ta yi Allah-wadai da kisan manoma 40
CUPP ta bayyana kisan gillar da ake zargin ‘yan Boko Haram sun yi wa manoma 40 a jihar Borno a matsayin alama mai tayar da hankali game da gazawar gwamnati wajen cika alkawarin tsaro ga ‘yan ƙasa.
Sanarwar ta CUPP ta jaddada cewa matsalar tsaro ta ƙara ta'azzara a jihohi daban-daban, inda aka rasa rayuka sama da 1,000 a ‘yan shekarun nan kuma miliyoyin mutane sun rasa matsugunansu.
CUPP ta ce hare-haren ‘yan ta’adda, garkuwa da mutane da kuma sauran laifukan da suka shafi tsaro sun zama ruwan dare gama gari.
CUPP: 'Alamu sun nuna gwamnatin APC ta gaza'
A cewar babbar kungiyar ƴan adawar, hakan na nuni da gazawar gwamnatin APC wajen aiwatar da tsare-tsaren tsaro yadda ya kamata.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa duk da biliyoyin Naira da aka kashe a fannin yaƙi da ta’addanci, babu wani sakamako da za a nuna a kasa.
Ta bayyana cewa gwamnati ba ta aiwatar da tsare-tsaren da za su kawo karshen matsalar ba, abin da ke barazana ga zaman lafiyar ƙasar baki ɗaya.
CUPP ta yi kira da a yi gyare-gyare na gaggawa a tsarin tsaron ƙasa, tana mai jaddada cewa akwai bukatar samun shugabanci na gari da zai iya magance wannan babbar matsala.
CUPP ta buƙaci ƴan Najeriya su yi watsi da APC
Ƙungiyar ta ce lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su yi fatali da jam’iyyar APC a babban zaɓen 2027, rahoton Guardian.
Ta yi gargadin cewa idan aka bar gwamnatin APC ta cigaba da mulki, za a iya fuskantar mummunan sakamako, ta ce ya kamata ƴan Najeriya su farka a 2027.
Mai magana da yawun CUPP, Mark Adebayo, ya yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a harin na jihar Borno.
Ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.
A cewarsa, babu wata al’umma da za ta ci gaba idan babu tsaro, kuma lokaci ya yi da za a mayar da hankali kan kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.
"Dalilin sukar tsarin Tinubu" - Gwamnan Bauchi
Kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi babu siyasa a yawan sukar da yake wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnan ya ce yana faɗawa shugaban ƙasa gaskiya ne game da tsare-tsaren da ya ɓullo da su waɗanda suka ƙara kuntatawa ƴan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng