'Yan Majalisa 12 na Shirin Ficewa daga Jam'iyyar PDP? Bayanai Sun Fito
- Jam'iyyar PDP reshen jihar Abia ta yi karin haske kan raɗe-raɗen da ke yawo cewa Ƴan majalisarta na jihar na shirin sauya sheƙa
- Shugaban PDP na Abia, Abraham Amah ya musanta jita-jitar da cewa wasu mara son zaman lafiya ne suka ƙirƙiro labarin da nufin tayar da rikici
- PDP dai na da ƴan Majalisa 12, mafi rinjaye a Majalisar dokokin jihar Abia yayin da LP mai mulki ƙe da ƴan Majalisu 11, sai APC mai kujera ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Shugaban PDP na jihar Abia, Abraham Amah, ya musanta rahotannin da ke cewa 'yan majalisar dokokin jihar na PDP na shirin ficewa daga jam'iyyar.
PDP ce jam'iyyar da ke da mafi rinjaye a Majalisar dokokin jihar Abia, inda take da ƴan Majalisa 12.
Jam'iyya mai mulkin Abia watau LP na da ƴan Majalisa 11, sai kuma APC mai adawa da ke da ɗan majalisa 1, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan Majalisa 12 na shirin ficewa daga PDP?
Abraham Amah ya karyata rahotonnin da ake yaɗawa cewa duka ƴan Majalisar PDP guda 12 a jihar Abia na shirin barin jam'iyyar zuwa wata daban.
Amah ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsakin PDP na mazaɓar Abia ta Arewa da aka gudanar a Ozu Abam, karamar hukumar Arochukwu.
Ya ce wannan jita-jita ba gaskiya ba ce kuma ya kamata a yi watsi da ita. Ya danganta rahoton da "masu neman tayar da zaune tsaye" da ke yada labaran karya.
Tsohon ɗan Majalisa ya yi martani kan batun
A nasa bangaren, tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar Arochukwu/Ohafia, Uko Nkole, ya ce wannan rahoto abin dariya ne kuma ya kira shi da "shagala kawai."
Ya yi kira ga 'yan majalisar da mambobin jam'iyyar su ci gaba da jajircewa wajen gyara da farfaɗo da PDP domin tunkarar zabukan gaba, rahoton Vanguard.
Hon. Nkole ya jaddada cewa duk da jam'iyyar PDP ta koma tsagin 'yan adawa, har yanzu tana da mambobi masu inganci, nagarta da jajircewa, wanda ke nuna jam'iyyar na da tubali mai karfi a Abia.
Har yanzu jam'iyyun siyasa na tsoron PDP
A nasa jawabin, sakataren yada labaran PDP, Eric Ikwuagwu, ya ce har yanzu jam'iyyarsu ce kaɗai ke ba duk wasu ƴan siyasa tsoro da fargaba saboda mabiyan da take da su a Abia.
Ya kwatanta PDP da itace mai fitar da ganye a lokacin rani domin ba da damar da sababbin ganye za su fito, ya tabbatar da cewa "daga yanzu, dimokuradiyya ta cikin gida za ta yi tasiri a jam'iyyar."
Shugaban PDP na yankin kuma tsohon shugaban karamar hukumar Bende, Gabriel Elendu, ya bayyana cewa taron yana da matuƙar muhimmanci wajen ci gaban jam'iyyar.
PDP ta ɗauro ɗamarar karɓe mulki a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa sakataren jam'iyyar PDP ya yi ikirarin cewa sun shirya tsaf domin karɓe mulki daga hannun APC a zaɓen 2027 da ke tafe.
Sanata Samuel Anyanwu, wanda kotu ta sauke daga kujerar sakataren, ya ce yana nan daram a kujerarsa kuma PDP za ta ba APC mamamki a babban zaɓe na gaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng