Gwamna Ya Samo Tallafin Naira Biliyan 1.3 daga Ƙungiyoyin Duniya, Kuɗin Sun Ɓace

Gwamna Ya Samo Tallafin Naira Biliyan 1.3 daga Ƙungiyoyin Duniya, Kuɗin Sun Ɓace

  • Hukumar EFCC ta cafke jami'ai biyar na hukumar tattara kudin haraji ta jihar Katsina bisa zargin karkatar da kimanin N1.3b
  • Gwamnatin Katsina ce ta kai ƙorafin mutane biyar ɗin hukumar EFCC bayan an nemi kuɗin an rasa a tsakaninsu
  • Kungiyar lafiya ta duniya watau WHO da wata ƙungiyar ALIMA ne suka ba da tallafin kuɗin kuma aka ajiye su a baitul-mali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) sun kama ma’aikata biyar na hukumar tara haraji ta jihar Katsina bisa zargin satar naira biliyan 1.3.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an da aka kama sun haɗa da Rabiu Abdullahi, Sanusi Mohammed Yaro, Ibrahim M. Kofar Soro, Ibrahim Aliyu, da Nura Lawal Kofar Sauri.

Hukumar EFCC.
EFCC ta tsare jami'an gwamnatin Katsina da ake zargi da karkatar da tallafin WHO kimanin N1.3bn Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Rahoton da Daily Trust ta wallafa ranar Litinin, 13 ga watan Janairu, 2025 ya nuna cewa an kama su ne a ƙarshen makon d ya wuce.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Mutanen gari sun yi tara tara, sun kama babban mawaƙi ɗauke da kan mace

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta kama jami'an gwamnatin Katsina

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da kamen nasu a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa adadin kuɗin da ake zargin jami'an gwamnatin su biyar sun karkatar ya kai N1,294,337,676.53.

Oyewale ya ce EFCC ta cafke waɗanda ake zargin ne biyo bayan ƙorafin da gwamnatin jihar Katsina ta shigar.

Gwamnatin Katsina ta kai ƙorafi ofishin EFCC

Gwamnatin Katsina ta yi zargin cewa waɗanda ake zargin sun haɗa baki suka wawushe maƙudan kuɗaɗen sama da Naira biliyan ɗaya.

A cewarsa, kudin sun shiga asusun gwamnatin jihar daga ƙungiyar lafiya ta duniya watau WHO da kungiyar ALIMA ta ƙasa da ƙasa.

Hukumar EFCC ta binciko wasu bayanai

"Binciken farko da EFCC ta gudanar ya nuna cewa Rabiu Abdullahi, tsohon darakta a hukumar, wanda yanzu shi ne babban sakatare shi ya sa aka buɗe asusu da sunan Boirs a bankin Sterling."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi magana kan kisan manoma 40, ta fadi abin da ya faru

"A cikin asusun, ya sanya daraktan asusun tattara haraji, Sanusi Mohammed Yaro da Ibrahim M. Kofar Soro, a matsayin waɗanda za su iya sa hannu a cire kuɗaɗen."
"Bincike ya nuna cewa Nura Lawal da kamfaninsa na “NADIKKO” da su ake amfani wajen karkatar da kudaden da aka sace.

- Dele Oyewale.

Wane mataki EFCC za ta ɗauka?

Hukumar EFCC ta ce a halin yanzu ana ci gaba bincike don gano dukkan bayanan da ke da alaƙa da lamarin, tare da tabbatar da cewa waɗanda ake zargi sun fuskanci shari’a.

Kakakin EFCC ya ce an tsare wadanda ake zargin ne a ofishin hukumar da ke Kano, inda ya ce za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.

EFCC ta cafke jami'anta guda 10

A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta turke wasu daga cikin jami'anta sakamakom ɓatan wasu kayayyaki a hannunsu.

Kara karanta wannan

Cire tallafin fetur ya fara haifar da sauƙi ga talakawa, cewar hadimin Tinubu

A cewar hukumar, tsare jami'an da aka yi na daga cikin binciken cikin gida da ake gudanarwa domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262