"Ina da Alaƙa da Tinubu," Gwamna na 4 da Ake Zargin Yana Shirin Komawa APC Ya Yi Magana

"Ina da Alaƙa da Tinubu," Gwamna na 4 da Ake Zargin Yana Shirin Komawa APC Ya Yi Magana

  • Gwamnan Osun, Ademola Adeleke ya ce zama daram a jam'iyyar PDP domin babu wani shiri da ya yi na sauya sheƙa zuwa APC
  • Mai magana da yawun gwamnan Osun, Olawale Rasheed ya ce Gwamna Adeleke na da kyayyawar alaƙa da shugaban ƙasa, Bola Tinubu
  • Ya ce APC ce ta kirkiro wannan ƙaryar take yaɗawa saboda ta fara gane cewa ba za ta iya kayar da Gwamna Adeleke ba a zaɓen 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya musanta rahotannin da ake yaɗawa cewa yana shirin ficewa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mallam Olawale Rasheed, ya fitar, ya bayyana raɗe-raɗin a matsayin ƙarya da ƙage mara tushe balle makama.

Gwamna Adeleke na Osun.
Gwamna Adeleke ya musanta jita-jitar cewa yana shirin barin PDP zuwa APC Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Rasheed ya bayyana cewa babu wani yunƙuri ko da sau ɗaya da Gwamna Adeleke ya yi nufin barin PDP zuwa APC, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'PDP za ta kwace mulki a hannun APC a zaben 2027,' Sakataren jam'iyya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Adeleke na shirin shiga APC?

A cewarsa, wannan jita-jitar da aka ƙirƙiro ta nuna a fili cewa jam'iyyar APC ta tsorata, ba za ta iya kai labari ba a zaɓen gwamnan Osun da za a yi a 2026.

"Babu wani shiri ko yunƙuri da Gwamna Adeleke ya yi da nufin komawa APC. Muna tausaya wa APC bisa ga matsalolin da take fuskanta wanda ya sa ta fara hangen ba za ta kai labari ba.
"A bayyane yake babu wani ɗan takara da zai iya kayar da Gwamna Adeleke, wannan ya sa APC ta rikice ta rasa mafita."

APC ta fara hango rashin nasara a 2026

Kakakin gwamnan Osun ya kara da cewa ga dukkan alamu APC ta rasa wanda za ta ba tikitin takarar da zai ya karawa da Ademola Adeleke.

A rahoton Daily Post, Rasheed ya ci gaba da cewa:

"Jita-jitar nan ta nuna yadda APC ke cikin matsalar rashin samun 'yan takarar da za su iya yin nasara a zaɓen gwamna na 2026.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa mai sukar kudirin harajin Tinubu ya sauya ra'ayi, ya fadi dalili

"Sun fahimci cewa tsohon gwamna ba zai iya yin nasara ba, kuma suna cikin rikici kan zaɓin 'dan takara.

Gwamna Adeleke ya zama na huɗu a PDP da a kwanan nan ake jita-jitar za su iya komawa APC bayan gwamnonin jihohin Enugu, Filato da Delta.

Gwamnan Osun yana da alaka mai kyau da Tinubu

Rasheed ya jaddada cewa Gwamna Adeleke yana da kyakkyawar dangantaka da shugaba Bola Tinubu.

Ya ce gwamnan jihar Osun na goyon bayan tsare-tsaren gyara tattalin arzikin ƙasa wanda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ɓullo da su.

"Gwamna Adeleke ya yi imani da cewa nasarar Shugaba Tinubu ita ce nasarar duk 'ya'yan Yoruba da kuma 'yan Najeriya masu kishin ƙasa. Don haka, goyon bayan shugaban ƙasa wajibi ne a gare shi," in ji Rasheed.

A ƙarshe, Olawale Rasheed ya yi kira ga jam'iyyar APC da ta daina yaɗa ƙarya domin hakan ba zai canza komai daga matsalolin da take ciki ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Gwamna Abba ya fadi abin da yake ci masa tuwo a kwarya kan tazarce

"Ba laifi ba ne idan APC ta Osun ta fasa tsayar da ɗan takara a 2026, domin babu wanda zai iya kayar da Gwamna Adeleke, in ji shi.

PDP ta musanta batun sauya shekar gwmna

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Delta ta musanta rahoton da ake cewa Gwamna Sherrif Oborevwori ya gama shirin shiga APC.

PDP ta bayyana cewa jita-jitar mugunta ce kawai amma mai girma gwamnan Delta yana nan daram a jihar Delta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262