Tun kafin 2027, PDP Ta Haramta Wa Kowa Neman Takara, Ta Tsayar da Gwamna ba Hamayya

Tun kafin 2027, PDP Ta Haramta Wa Kowa Neman Takara, Ta Tsayar da Gwamna ba Hamayya

  • Duk da sauran lokaci da ya rage a fara shirye-shiryen zaben shekarar 2027, jam'iyyar PDP ta yi wa gwamna gata
  • Jam’iyyar PDP ta jihar Akwa Ibom ta zabi Gwamna Umo Eno a matsayin dan takararta tilo na zaben gwamna a shekarar 2027
  • PDP ta bayyana cewa zaɓen Gwamna Eno ya biyo bayan kyakkyawan shugabancinsa da kuma tasirin shirinsa mai suna "Arise Agenda."
  • Wannan matakin ya kawar da duk wata yiwuwar fafatawa ko takarar wasu masu neman kujerar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Akwa Ibom

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Uyo, Akwa Ibom - Duk da cewa saura fiye da shekaru biyu kafin babban zaɓe a Najeriya, jam’iyyar PDP ta fitar dan takarar gwamna a Akwa Ibom.

Jam'iyyar reshen jihar ta zabi Gwamna Umo Eno a matsayin dan takararta tilo na zaben gwamna na shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Abin na gida ne: Kanin tsohon gwamna ya shirya neman kujerar yayansa da ya bari

Tun yanzu PDP ta tsayar da dan takarar gwamna
Jam'iyyar PDP ta haramta wa sauran yan siyasa neman kujerar gwamna a Akwa Ibom. Hoto: Pastor Umo Eno.
Asali: Facebook

PDP ta tsayar da dan takara a 2027

Kakakin PDP a jihar Akwa Ibom, Edwin Ebiese, shi ya wallafa wannan sanarwa a shafin Facebook dinsa ranar Lahadi, 12 ga Janairun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ebiese ya ce jam'iyyar ta dauki wannan mataki duba da ƙoƙarin inganta Akwa Ibom da gwamnan ke yi ta ɓangarori da dama.

Gwamnatin Umo Eno ya kai shekara ɗaya da watanni shida wanda aka rantsar da shi a matsayin gwamnan Akwa Ibom ranar 29 ga Mayun 2023.

A cikin sanarwar da shugaban PDP na jihar, Aniekan Akpan, ya sa hannu, ya gwamnan ya cancanci haka duba da inganta rayuwar al'umma.

"Bayan muhawara a taron jam’iyyar PDP na jiha wanda aka yi ranar 6 ga Janairu, 2025, a hedikwatar jam’iyyar, jam’iyyar ta amince da Pastor Umo Bassey Eno a matsayin dan takararta tilo na zaben gwamna na 2027."
“Shugabancinsa na koyi da hangen nesansa, kamar yadda aka tsara a cikin shirin Arise Agenda, ya kawo gagarumin ci gaba a jihar Akwa Ibom."

Kara karanta wannan

'Mun gano shi': Shugabannin PDP sun tabbatar gwamna zai koma APC, sun jero dalilai

- Aniekan Akpan

Musabbabin tsayar da Gwamna Eno takara

Da wannan mataki, jam’iyyar PDP ta dakatar da duk wani yiwuwar takarar wasu ‘yan jam’iyya da kuma kawar da fafatawa kafin zaben 2027.

Jam’iyyar ta ce wannan shawara ta biyo bayan "kyakkyawan shugabancin" da gwamnan ke yi ga al'ummar jihar.

Shirinsa na 'Arise Agenda' shi ne tsari na Gwamna Eno na bunkasa tattalin arzikin jihar Akwa Ibom.

Gwamna Eno ya ziyarci hedikwatar PDP a Uyo ranar Asabar 11 ga watan Janairun 2025 sa’o’i kadan bayan ya rusa majalisar zartarwarsa.

Gwamna ya gargadi masu kamun kafa a gwamnatinsa

Kun ji cewa Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom ya karyata jerin sunayen kwamishinoni da aka wallafa, ya ce jerin ba gaskiya ba ne.

Gwamna Eno ya bayyana cewa mako mai zuwa zai gabatar da jerin sunayen gaskiya ga Majalisar Dokokin Jihar Akwa Ibom don tantancewa.

Gwamnan ya gargadi masu neman shiga majalisar zartarwa da kada su nemi matsayi ta hannun wasu mutane don ba su dama, ya ce hakan ba zai yi tasiri ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.