Wike Ya Fusata, Ya Yi Wa Ministan Buhari Wankin Babban Bargo

Wike Ya Fusata, Ya Yi Wa Ministan Buhari Wankin Babban Bargo

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesome Wike ya caccaki tsohon ministan matasa da wasanni wato Solomon Dalung
  • Ministan ya ce Dalung bai yi wata rawar a zo a gani ba a yayin da yake riƙe da muƙamin minista a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari
  • Wike ya kuma bayyana cewa Dalung ba zai yaba ayyukan ci gaban da suke yi ba saboda ƙiyayyarsa gareshi da kuma ga Shugaba Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki Solomon Dalung wanda ya yi aiki a gwamnatin Muhammadu Buhari.

Nyesom Wike ya caccaki Dalung inda ya bayyana cewa bai taɓuka komai ba a muƙamin ministan da ya riƙe a lokacin Muhammadu Buhari.

Ministan birnin tarayya Abuja ya yi wa Solomon Dalung wankin babban bargo
Wike ya caccaki tsohon ministan Buhari Solomon Dalung. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike/ Solomon Dalung
Asali: Facebook

Wike ya zargi Solomon Dalung da nuna ma sa ƙiyayya

Kara karanta wannan

Menene gaskiyar labarin DSS sun kama Peter Obi? tsohon gwamnan ya fede gaskiya

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Lere Olayinka, ya fitar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya yi wa tsohon ministan wasannin martani ne kan iƙirarin da ya yi na cewa gina hanyoyi a babban birnin tarayya Abuja ba ci gaba ba ne.

A cikin sanarwar ministan ya ce ƙiyayyar Solomon Dalung a gare shi da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, ta sanya ya makance daga amsar gaskiya, rahoton The Punch ya tabbatar.

Wike ya ce Dalung bai taɓuka komai ba

Ministan ya kuma bayyana cewa Solomon Dalung bai yi wata rawar a zo a gani ba a yayin da yake minista a gwamnatin Buhari, wannan ne ya sa baya iya ganin alfanun abinda suke yi a yanzu.

"Dalung, wanda a lokacin yana a matsayin ministan matasa da wasanni ya kasance bai taɓuka komai ba, har ya kai ga cewa yin tituna da gyaransu ba za a iya ɗaukarsa a matsayin ci gaba ba, saboda wasu ƴan Najeriya ba su da motoci."

Kara karanta wannan

Kaduna: Sanatan PDP ya yi martani kan shirin yi masa kiranye daga majalisa

“Ga mutumin da a ƙarƙashin jagorancinsa Najeriya ta kasa samun damar zuwa gasar cin kofin Nahiyar Afrika sau da dama, tituna kawai na da amfani ga ƴan Najeriya masu motoci. Wannan wane irin tunani marar tushe ne wannan!"
“A tunani irin na Dalung, waɗannan hanyoyin da ake ginawa a garuruwan da ke kusa da Abuja irin su Kabusa, Ketti, Takushara da kuma hanyar Lokoja mai haɗawa da Pia ba za su taimaka wajen ci gaba ba idan aka kammala su."
“Duk da haka, ba abin mamaki ba ne domin daman babu abin da ya iya sai kalamai marasa kan gado."
"Misali a lokacin da yake minista, yayin da aka samu jinkiri wajen biyan alawus-alawus na tawagar Super Falcons yayin gasar cin kofin mata ta Afrika a Ghana a shekarar 2016, ya yi katoɓarar cewa ba a san za su yi nasara ba shiyasa ba a yi shirin da ya dace ba."

Kara karanta wannan

Abuja: Bincike ya yi nisa, an gano wanda ya tashi bom a makarantar Islamiyya

"A lokacin wasannin Olympics na Rio 2016, lokacin da ma’aikatar wasanni ta kasa sakin kuɗi don shirin tawagar ƴan kwallon kafa, ya ce, ‘Wa ya kai su can? Me suka je yi? Saboda suna ƙarƙashin shekara 23 kuma suka tafi Amurka. Yanzu sun samu matsala, ta ya hakan ya zama damuwarmu?’
"Saboda haka, ba abin damuwa ba ne idan irin wannan mutum ya yi magana da rashin hikima. Abin da ya kamata ƴan Najeriya, musamman waɗanda suke kusa da shi, su kula da shi, shi ne lafiyar kwakwalwarsa, wacce ke bayyana alamun buƙatar taimako cikin gaggawa."

- Nyesom Wike

An ƙalabulanci Tinubu kan tallafin man fetur

A wani rahoto da Legit NG ta wallafa, sanatoci sun nuna damuwarsu kan yadda aka gudanar da kasafin kuɗin shekarar 2024 da ta gabata, inda suka buƙaci gwamnati ta yi mu su bayani kan batun kuɗin tallafin da aka cire.

Wasu daga cikin sanatocin sun koka kan sabon tsarin aiwatar da kasafin kuɗi da gwamnatin Shugaba Tinubu ta zo da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng