Babban Jigon PDP kuma Fitaccen Ɗan Kasuwa da Magoya Baya 6,000 Sun Koma APC
- Jam'iyyar APC ta ƙara samun ƙaruwa a jihar Abia da ke Kudu maso Gabashin Najeriya bayan sauya sheƙar tsohon shugaban PDP
- Wani ƙusa a PDP kuma fitaccen ɗan kasuwa a Abia, Cif Kelvin Jumbo Onumah ya jagoranci dubannin magoya bayansa, sun koma jam'iyyar APC
- Shugaban APC na Abia, Dr. Kingsley Ononogbu ya karɓi masu sauya sheƙar hannu bibbiyu, ya ce da wannan jam'iyyar ta shirya tsaf don karɓe mulki a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Babban jigo a jam'iyyar PDP ta jihar Abia kuma fitaccen ɗan kasuwa a fannin man fetur da iskar gas, Cif Kelvin Jumbo Onumah, ya sauya sheƙa zuwa APC.
Fitaccen ɗan siyasar a Kudu maso Gabashin Najeriya ya fice daga PDP zuwa APC ne tare da magoya bayansa 6,000.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa an tarbe shi a hukumance a ranar Juma'a, 10 ga Janairu, 2025, a filin wasa na Abiriba da ke karamar hukumar Ohafia ta jihar Abia
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban APC reshen jihar Abia, Dr. Kingsley Ononogbu, ya mika masa tutar jam'iyyar a hukumance a wurin taron.
Wannan na zuwa ne bayan tsohon shugaban PDP na Abia, Sanata Emma Nwaka da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Chinedum Orji sun koma APC.
Jiga-jigan sun koma jam'iyyar APC ne tare da hadiman tsohon gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu.
APC ta shirya karɓe mulkin jihar Abia
A jawabinsa, Dr. Ononogbu ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta shirya tsaf don karɓar mulkin jihar Abia a zaɓen 2027.
Ya ce APC za ta yi amfani da nasarorin da Sanata Orji Uzor Kalu, mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, da ƙaramar ministar ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha, suka cimma a yaƙin neman zaɓe.
Dalilin jigon PDP na komawa APC
Chief Onumah ya bayyana cewa ya yanke shawarar shiga jam'iyyar APC ne domin kawo ci gaba ga mutanensa na mazabar Arochukwu/Ohafia da kuma yankin Abia ta Arewa baki ɗaya.
Ɗan siyasar ya ƙara da cewa ya shiga APC ne domin ba da tashi gudummuwar wajen kawo ci gaba ga al'umma a Abia da ƙasa baki ɗaya.
Ana ganin dai shekar da manyan ƴan siyasa ke yi zuwa APC a jihar Abia na ƙarawa jam'iyyar ƙarfi da tasiri tun bayan zaɓen 2023.
Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Abia ta fara shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027 mai wanda wanda shugabanninta ke nanata cewa za su karɓe mulki daga LP.
Tsohon shugaban AMAC ya koma APC
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban ƙaramar hukumar kwaryar birnin Abuja (AMAC), Prince Nicholas Ukachukwu ya sauya sheka zuwa APC.
Ya kuma bayyana burinsa na tsayawa takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan Anambra da za a yi a watan Nuwamba, 2025.
Asali: Legit.ng