"Burinmu Gyara Najeriya": Shugaban SDP Ya Fadi abin da Suka Tattauna da El Rufai

"Burinmu Gyara Najeriya": Shugaban SDP Ya Fadi abin da Suka Tattauna da El Rufai

  • Shugaban SDP, Shehu Gabam, ya kare tattaunawarsa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, yana mai cewa ba laifi ba ne ganawarsu
  • Gabam ya yi mamakin yadda ganawarsu da El-Rufai ta hana wasu sakat, inda ya ce gwamnati ba ta san darajar tsohon gwamnan ba
  • Shugaban jam'iyyar adawar ya ce ministocin Bola Tinubu ba su da zalakar gudanar da ayyuka yayin da tattali ke kara tabarbarewa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Gabam, ya bayyana zantukan da suka yi da jigon jam’iyyar APC, Nasir El-Rufai.

Shehu Gabam ya ce jam’iyyarsa ta SDP ba ta yi wani laifi ba wajen tattaunawa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, El-Rufai.

Shugaban SDP ya fadi abin da suka tattauna da El-Rufai a gabawarsu
Anji abin da El-Rufai da shugabannin adawa suka tattaunawa a ganawarsu. Hoto: @IU_Wakilii
Asali: Twitter

"Me ya sa ake ce-ce-ku-ce?' - Shugaban SDP

Shugaban SDP ya bayyana hakan ne lokacin da ya bayyana a shirin 'Siyasa a yau' na gidan talabijin din Channels a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

'Ko a jikinmu': Gwamnan APC kan hadakar jam'iyyun adawa, ya fadi dabarbarun da za su yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Me yasa ake ce-ce-ku-ce kan Malam Nasir El-Rufai? Idan ba shi da muhimmanci, me ya sa ake damuwa da abin da ya yi? Me ya sa ake damuwa da Segun Sowunmi?
"Idan suna da mahimmanci, me yasa gwamnati ba za ta ba su ayyukan da suka dace da su domin inganta aikinta ba?"

- Shehu Gabam ya tambaya.

Dalilin ganawar El-Rufai da shugaban SDP

Shehu Gabam ya kara da cewa:

"Mun yi taro ne don nazarin halin da kasar nan ke ciki a shekarar 2024, da duba inda abubuwa ke tafiya ba daidai ba."

Shugaban jam'iyyar ta SDP ya ci gaba da cewa:

“Mu jam’iyyar adawa ce da ke da zababbun ’yan majalisar tarayya, majalisun jihohi, da kuma a kananan hukumomi.
“Don haka wajibi ne a matsayinmu na jam’iyya mu duba wurare da abubuwan da ba su tafiya daidai, sannan mu bude dama a jam’iyyar don jama'a su shigo."

Shehu Gabam ya kuma ce bai kamata wannan ganawar ta zamo abin ce-ce- ku-ce ba domin:

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi alakarsa da El-Rufai, ya magantu kan barinsa APC da hana shi Minista

"Haka APC ta yi a lokacin da jam'iyyar PDP ke tafiyar hawainiya a mulkinta; suka sake tsara kansu, suka yi hadin gwiwar da ya kai ga kayar da PDP."
"Don haka ba mu yi wani abu da ba daidai ba. Wannan ba shi ne karo na farko da El-Rufai ko Segun Sowunmi suka zo wurina ba."

Ya ce: "Manufar mu ita ce gyara Najeriya, ba yi wa Najeriya zagon kasa ba."

Shugaban SDP ya caccaki ministocin Tinubu

Shugaban jam'iyyar na SDP ya ce ministocin gwamnatin Bola Tinubu ba su da kwarin gwiwar cimma burin shugaban kasar.

Shehu Gabam ya ce Najeriya na fama da matsalar tattalin arziki fiye da kowanne lokaci a baya.

"Babu shugaban da zai yi nasara idan shekaru biyu na farkon mulkinsa suna cike da matsaloli. Jonathan ya fadi zabe saboda irin wannan dalilin."

- Shehu Gaban.

El-Rufai ya gana da Almustapha, shugaban SDP

Tun da fari, mun ruwaito cewa manyan 'yan siyasa sun gana a Abuja yayin da ake ta hasashen hadakar jam'iyyun adawa a Najeriya don tsara manufofi na gaba.

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, Manjo Hamza Al-Mustapha, da jagororin SDP da PDP sun tattauna kan yanayin kasa da zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.