Zaben 2027: Gwamna Abba Ya Bayyana Abin da Yake Ci Masa Tuwo a Kwarya kan Tazarce
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan shirinsa dangane da sake neman zaɓe a shekarar 2027
- Abba ya bayyana cewa a yanzu batun yin tazarce bai damunsa domin ya maida hankali ne wajen sauke nauyin da aka ɗora masa
- Gwamnan ya ce Allah ne Ya ƙaddara zai zama gwamna, kuma idan Ya so zai sanya ya ƙara riƙe madafun ikon jihar a karo na biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan neman tazarce a zaɓen shekarar 2027.
Gwamna Abba Kabir ya bayyana cewa ko kaɗan batun sake lashe zaɓe a zaɓen 2027 ba ya damunsa.
Gwamna Abba ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana wajen ba da tallafi ga mata na wata-wata a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba bai damu da wa'adi na biyu ba
Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ba zai damu kansa ba kan zaɓen 2027, saboda ya san cewa Allah ne yake ba da mulki.
Gwamnan ya yi kira da a guji furta kalaman ƙiyayya da tunzura jama’a yayin shirin zaɓen 2027.
A cewar gwamnan, irin waɗannan kalaman tunzura jama'a na iya tsoratar da masu zaɓe da suke son zuwa kaɗa ƙuri'unsu.
Idan ba ku manta ba dai jam’iyyar APC ta sha kayen ban mamaki a hannun NNPP a zaɓen shekarar 2023 da ya gabata.
APC ta rasa kujerar gwamna, kujeru biyu na Sanata, da kujeru 18 cikin 26 na majalisar makilai, da kuma kujeru 26 cikin 40 na majalisar dokokin jiha.
Me Gwamna Abba ya ce kan tazarce?
"Ba tazarce ba ne abin da na damu da shi. Na fi maida hankali a kan samar da romon dimokuraɗiyya da sauke nauyin da aka ɗora min a wannan wa'adin na farko."
"Ina son al’ummar Kano su yi min alƙalanci bisa ga abin da na cimma a ƙarshen wannan wa’adi."
“Mun san waɗannan mutanen waɗanda aka yi fatali da su sosai a 2019 da 2023. Mun yi nasara a kansu a lokacin da ba mu da wata kujera ta siyasa, ko da ta Kansila. Amma Allah Ya sa mun yi nasara da ƙuri’u masu rinjaye."
“Allah ne Ya ƙaddara zan zama gwamna. Na yi imani cewa idan Allah Ya ƙaddara zan yi wa’adi na biyu, zan yi. Idan kuma ba haka ba, ba zan yi ba. To, me ya sa zan damu kaina?"
- Gwamna Abba Kabir Yusuf
Haka kuma, gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda maƙiya Kano da suke fakewa da adawa, ke ƙoƙarin tayar da tarzomar siyasa a jihar.
Gwamna Abba ya yi wa APC martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano na jam'iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, ya yi wa APC martani kan shirinta na karɓe ikon jihar.
Abba Kabir Yusuf ya tunatar da APC cewa Allah ne yake ba da mulki ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so, ba wayau ko dabarar mutum ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng