Ganduje Ya Karbawa Kakakin APC da za a 'kashe' Fada, Ya Zafafa Kalamai ga Obi
- Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya bayyana goyon bayansa ga mai magana da yawun jam’iyyar, Felix Morka kan barazanar kisa
- Abdullahi Ganduje ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi da harzuka magoya bayansa domin cin mutuncin Morka
- Ganduje ya ce APC za ta ci gaba da kare gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu daga duk wani zargi mara tushe da 'yan adawa ke mata a kasar nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya fito fili ya goyi bayan mai magana da yawun jam’iyyar, Felix Morka, bayan masa barazanar kisa har sau 200.
Rahotanni na nuni da cewa Abdullahi Umar Ganduje ya yi zargin cewa barazanar ta samo asali ne daga magoya bayan Peter Obi.
Punch ta wallafa cewa Ganduje ya bayyana cewa kalaman Obi sun zama wata hanyar da ta sa magoya bayansa suka rika cin mutuncin Morka da iyalansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin Ganduje ya biyo bayan wata hira da Morka ya yi da Arise Television inda ya yi wasu kalamai da suka tayar da kura a tsakanin magoya bayan Obi.
Barazanar kisa ga Morka da iyalansa
Morka ya yi zargin cewa ya samu barazanar kisa daga magoya bayan Peter Obi bayan da ya ce Obi ya wuce gona da iri wajen sukar gwamnatin Bola Tinubu.
A hirar da ya yi, Morka ya zargi Obi da yada kalamai da ke haifar da rikici tare da yin kira ga gwamnati da ta dauki matakin kare kanta.
Peter Obi ya mayar da martani ta hanyar tambayar ‘yan Najeriya ko sukar gwamnatin Tinubu na nufin ya yi wani abu da ya saba doka. Wannan ya kara tayar da kura a shafukan sada zumunta.
Ganduje ya karbawa Morka fadansa da Obi
Abdullahi Ganduje ya yi Allah-wadai da kalaman Obi, yana mai cewa suna da nasaba da tayar da hankali da yin barazana ga rayuwar Morka da iyalansa.
A cewar Ganduje;
“Bayan yin zargin karya na cewa Morka ya yi masa barazanar kisa, Obi ya jawo cin mutuncinsa a idon duniya, kuma ya tada magoya bayansa wajen yi masa barazanar kisa.”
Ganduje ya kuma kare Morka kan kalamansa a lokacin hirar, yana mai cewa ba su da wata alaka da barazana ga Obi ko wani mutum.
Maganar cigaba da kare gwamnatin Tinubu
Shugaban APC ya kara da cewa jam’iyyar za ta ci gaba da mayar da martani kan duk wani zargi mara tushe da ake yi wa gwamnatin Tinubu.
Shugaban jam'iyyar ya ce;
“Shin Obi yana tsammanin za mu zuba ido mu kyale ‘yan adawa su yada karya ba tare da mayar da martani ba?”
Ganduje ya jaddada cewa jam’iyyar APC ba za ta yi kasa a guiwa wajen kare mutuncin gwamnatin Tinubu daga duk wani yunkuri na bata suna.
APC ta kare Tinubu daga zargin rashawa
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC rashen Amurka ta yi Allah-wadai da ba Bola Tinubu lambar rashawa ta uku a duniya.
Jam'iyyar APC ta ce akwai makarkashiyar neman bata suna ga shugaban kasar a duniya duk da ayyukan alheri da yake shimfidawa a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng